Taraba: Masu garkuwa da mutane sun karbi Miliyan 20, sun saki Aminu Fika

Taraba: Masu garkuwa da mutane sun karbi Miliyan 20, sun saki Aminu Fika

Alhaji Aminu Jika, ya fito daga hannun masu garkuwa da mutanen da su ka tsare sa a jihar Taraba. Aminu Jika ya rike shugaban ma’aikatan gidan gwamnati a lokacin Danbaba Suntai.

Daily Trust ta bada rahoton cewa an saki wannan Bawan Allah ne bayan kwanaki 5 da tsare sa. Sai da Iyalinsa su ka biya makudan kudi sannan, tsohon Jami’in gwamnatin ya samu ‘yanci.

Rahotanni sun bayyana cewa Iyalin Aminu Jika sun biya Naira miliyan 20 kafin su fanshi Mai gidan na su. Dama can wannan ne adadin kudin da wadanda su ka sace shi su ka nema.

Miyagun sun tuntubi Iyalin tsohon COS na jihar Taraban a wayar salula, inda su ka hakikance a kan cewa sai an kawo masu miliyan 20 a cikin wani kungurmin daji sannan za su fito da shi.

KU KARANTA: 'Yan fashi sun hallaka wani Attajirin 'Dan Canjin kudi a Abuja

Haka kuma aka yi domin kuwa wani ‘Danuwan wanda aka sacen mai suna Nasiru Bobboji ya shaidawa ‘Yan jarida cewa an fito da Aminu Jika cikin tsakar-dare bayan an kai wannan kudi.

Alhaji Jika shi ne ya ke kula da harkokin gudanarwa a gidan gwamnati a lokacin da Marigayi Danbaba Suntai ya ke kan mulki. Suntai ya rasu ne bayan doguwar jinya a dalilin hadarin jirgi.

Idan ba ku manta ba, an bi Jika har gidansa ne da ke Unguwar Magami a babban birnin jihar Taraba na Jalingo, aka sace shi. An dauke tsohon Jigon gwamnatin ba tare an kashe kowa ba.

Jami’an tsaro sun yi alkawarin ceto Aminu Jika. Kawo yanzu dai ba su sake cewa komai game da lamarin ba. Alhaji Aminu Jika ya na cikin ‘yan gaban-goshin gwamna mai-ci, Darius Ishaku.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Online view pixel