Tirkashi: An kama mai hakar kabari a makabarta da yake sayar da kokon kan mutane akan naira 6,000

Tirkashi: An kama mai hakar kabari a makabarta da yake sayar da kokon kan mutane akan naira 6,000

- Wani mutum mai hakar kabari da ya fada harkar siyar da kokon kawunan mutane ya shiga hannun ‘yan sanda

- Yana siyar da kokon kawunan mutanen a kan naira dubu shida kowanne daya, Murtala mai maganin gargajiya ne ke siya

- Mai maganin gargajiyar ya bayyana cewa, yana maganin kasuwa ne da shi. Ya na maida kokon gari ne don sha duk safiya

Wani mutum mai aikin hakar kabari, dubunshi ta cika bayan da yake siyar da kokon kan mutum a naira dubu shida. Kazeem Olarewaju na tsaron makabartar Unguwar Oke Sunna ne a Legas. Ya shiga hannu ne bayan da aka tabbatar da zargin da ake mishi na sayar wa matsafa kokon kan mutane a makabartar.

Kamar yadda Kazim Olarewaju ya bayyana, shekaru biyu kenan da ya fara wannan haramtaccen kasuwancin. A karo na farko ya siyar da guda biyu ne a naira dubu goma sha biyu. Yunkurin siyarwa a karo na biyu ne aka damke shi.

Ya ce, ya fara wannan haramtacciyar harkar ne bayan da ya hadu da wani mai siyar da maganin gargajiya mai suna Murtala Salami. Sun hadu ne bayan da mai maganin gargajiyar ya je birne wata ‘yar uwarshi.

Ya samu mai tsaron makabartar inda ya bayyana mishi yana da bukatar kokon kan mutum har guda biyu. Da farko ya turje, amma daga baya sai ya bada hadin kai. Ya biya shi dubu sha biyu, sannan ya bashi kokon kan mutane biyu.

KU KARANTA: Da duminsa: Buhari ya nada jarumin Kannywood Nura Hussain a matsayin kwamishinan hukumar alhazan Najeriya

Bayan wani lokaci ne, ya kara tuntubarshi da bukatar. Ya ciro kokon kan, amma kafin ya kai ga mai maganin gargajiyar, sai ‘yan sanda suka damkeshi.

Kamar yadda Murtala mai maganin gargajiya ya sanar, yana amfani da kokon kan mutum ne don maganin kasuwa. Yana dakawa ne ya mayar dashi gari, yana barbadawa a ruwan magani yana sha da safe kafin ya ci abinci.

Ya ce, a da kafin ya samu hada maganin, yana yin cinikin naira dubu talatin ne a rana. Amma a yanzu, yana kai dubu tamanin zuwa dari a kullum.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Legas, Bala Elkana ya tabbatar da aukuwar lamarin. Ya ce suna bincike ne kafin a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel