Bashin Najeriya ya tashi daga $10b zuwa $84b a karkashin Buhari – Falalu Bello

Bashin Najeriya ya tashi daga $10b zuwa $84b a karkashin Buhari – Falalu Bello

Shugaban jam’iyyar PRP na kasa, Falala Bello, ya ja kunne game da bashin da ke kan Najeriya a halin yanzu, wanda ya ce ya tashi daga Dala biliyan 10 zuwa 84 a gwamnatin Shugaba Buhari.

Alhaji Falalu Bello ya yi wannan jawabi ne wajen wata zantawa da ‘Yan jarida a cikin makon nan a Garin Abuja. Jaridar Daily Trust ta kawo wannan rahoto a Ranar 3 ga Watan Disamban 2019.

Bello ya ja-kunnen ‘Yan majalisar tarayya cewa ka da su sake su yi na’am da danyen rokon karbo aron kudi na Dala biliyan 29.9 da shugaban kasar ya ke neman yi, domin bashin kasar ya yi yawa.

Tsohon shugaban bankunan na Habib, Intercity da Unity Bank na kasar, ya kara da cewa idan har aka amince da karbar wannan aro, zai zama bashin da ke kan Najeriya ya haura Dala biliyan 100.

Lokacin da su ka shiga ofis a 2015, wannan gwamnati sun gaji bashin Dala biliyan 10 ne kurum, yanzu bashin kasar nan ya haura Dala biliyan 84, kuma babu wani abin nunawa a kasa.” Inji sa.

KU KARANTA: Bayan wasu tafiye-tafiye, Buhari ya koma bakin aiki a Abuja

Bayan batun bashi, shugaban jam’iyyar adawar ya yi kira ga gwamnatin tarayya ta daina kashe kudi kan tallafin man fetur, wanda a cewar ta, wasu tsiraru ne su ke morewa da sunan Talaka.

Bello ya ke cewa: “Mai girma Shugaban kasa, tallafin man da ka ce sata ce, kuma ka yi alkawarin dainawa, har gobe ya na nan, asali ma fiye da yadda ya ke a da, akwai bukatar a tsaida shi.”

Har ila yau, Bello ya yi kira ga wannan gwamnatin APC ta tsaida farashin kudin kasar waje. A cewarsa saida Dalar Amurka da ake yi a kan N305 ko N345 a wasu wuraren ba dabara ba ce.

‘Dan Masanin Zazzau ya nuna cewa shugaba Buhari ya gaza a sha’anin tsaro duk da nasarar Boko Haram saboda yadda ake garkuwa da mutane. A karshe ya ce APC za ta watse kafin zaben 2023.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

r

Source: Legit

Online view pixel