Hanyoyi 7 da mutum zai bi don inganta lafiyarsa lokacin sanyi

Hanyoyi 7 da mutum zai bi don inganta lafiyarsa lokacin sanyi

A kwanaki kalilan da suka gabata, yanayin sanyi ya fara juyowa a kasar nan. Sau da yawa sanyi na farawa daga watan Nuwamba ne zuwa watan Maris. Gari na cika da sanyi, bushewar gari da kuma iska da yammaci ko kuma safiya.

Kamar yadda Gurama Gurama, masani a fannin kiwon lafiya ya ce, danshi a gari a wannan yanayi kalilan ne. Hakan kuwa na sa kwayoyin cuta su yadu a gari.

Ya ce, mafi yawan cutukan da ke yawo a lokacin nan na sanyi sun hada da mura, asthma, tashin ciwon sikila, ciwon ido, lamoniya, bushewar fata, habo, hatsarurruka a titi da sauransu.

Gurama malami a tsangayar koyar da hada magunguna ta jami’ar jihar Gombe, yace za a iya kiyaye duk cutukan da sanyi ke tafe da shi ta hanyar bin wadannan dokoki. A hakan ne za a samu ingantacciyar lafiya har lokacin ya kare.

1. Sanya kaya masu kauri don samun dumi ga yara da kuma tsofaffi. Shan ruwa mai yawa, a kalla lita daya da rabi zuwa biyu a kowacce rana.

DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: Smart Adeyemi na APC ya samu kuri'u mafi rinjaye a zaben Kogi ta Yamma

2. Sanya magani ko gilashi don kare idanu da kuma abun rufe hanci da baki don kariya daga kura.

3. Shafa mai a jiki don hana bushewar fata.

4. Shafa mai a lebe da kuma kasan kafa, hakan yana hana wuraren fashewa.

5. Idan mutum na da cutar asthma, a rage shiga waje mai datti ko mai kura kuma a kasance da inhaler don halin ko ta kwana da mutum zai iya shiga.

6. A wanke danyen abinci kamar kayan marmari da na lambu kafin a ci don gujewa yaduwar kwayoyin cutuka.

7. Kada a raina atisaye komai kankantarsa. Yana taimakawa wajen narkar da kitse tare da tabbatar da jiki na aiki yadda ya dace. Hakan kuwa na samar da dumi wanda ke daidaita zafin jiki lokutan sanyi.

Gurama ya kara da shawartar mutane da su dinga kashe kayan wuta bayan amfani dasu. Kashe wutar girki zai yi amfani don gudun tashin gobara.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel