Na godewa Allah da ba a kashe ni a zaben nan ba inji Dino Melaye

Na godewa Allah da ba a kashe ni a zaben nan ba inji Dino Melaye

Sanata Dino Melaye, wanda ya wakilici yankin Yammacin jihar Kogi a majalisar dattawa ya yi magana jim kadan bayan an sanar da sakamakon zabensa da aka karasa a karshen makon nan.

Farfesa Jide Lawal wanda ya yi aiki a matsayin Malamin zabe ya sanar da cewa Smart Adeyemi ne ya yi nasara a zaben Kogi ta yamma. APC ta samu kuri’a 88,373, yayin da PDP ta tashi da 62,133.

Ina godewa Ubangiji Madaukaki da ya bani tsawon rayuwa bayan yunkuri 5 da aka yi na kashe a taron-dangin jami’an tsaro hukumar INEC, gwamnatin tarayya, jihohi da kanan hukumomi.

A Ranar Lahadin, Sanata Melaye ya sake fitowa dandalin Tuwita ya na cewa: “An yi fada da ni ta sama, kasa, ruwa da rauhanai. Ba batun zabe ake yi ba, maganar rayuwa ta ake yi. Nagode.”

KU KARANTA: Tarihin ‘Dan takarar APC da ya kawo karshen rawar Dino Melaye a Majalisa

Dino Melaye ya kara da cewa: “Kokarin da maza da matan duk fadin Najeriya, musamman ‘Yan Kogi ta Yamma su ka yi na zabe na, ya nuna cewa Ubangiji ya na tare da ni, da ku gaba daya.”

Dino ya kara da cewa: “Har gobe ni ba sa’ar Adeyami ba ne a siyasa. Nagode mutanen Najeriya.”

‘Dan majalisar ya ce: “Wadanda su ka nemi su ga baya na, ba su fi karfin Ubangiji ba. Ka da jama’a su damu da ni. Ina nan garau. Na godewa Ubangiji da ba ayi nasara yunkurin kashe ni ba.”

Dino Melaye ya kare da cewa lafiyayyen kare ya fi mushen doki. Suna na Dino ba zan kai kasa ba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel