Zamfara: An rufe Bello Dankande Gamji a gidan yari bisa zargin satar dabbobi

Zamfara: An rufe Bello Dankande Gamji a gidan yari bisa zargin satar dabbobi

A Ranar Laraba, 27 ga Watan Nuwamba, babban kotun shari’a da ke jihar Zamfara, ya nemi a garkame tsohon Kwamishinan kananan hukumomi da masarautun jihar, Bello Dankande Gamji.

Daily Trust ta rahoto cewa ana zargin Bello Dankande Gamji da hannu wajen satar wasu dabbobi. Alhaji Dankande Gamji ya rike mukami ne a gwamnatin da ta shude ta Alhaji Abdulaziz Yari.

Gwamnati ta hannun wani Lauyanta mai suna Barista Ibrahim Haruna, ta na tuhumar Dankande Gamji da taimakawa da kutun-kutun wajen sace wasu shanu 50 da tumaki 52 na jama’an jihar.

Ibrahim Haruna ya gabatar da hujjojinsa a gaban kotu ya na zargin tsohin Kwamishinan da ba wasu ‘yan banga; Saminu Gandau da Shitu Mafara, umarnin yin gaba da dabbobin wasu mutane.

Lauyan ya shaidawa kotu cewa a lokacin da Alhaji Dankande Gamji ya ke ofis, ya umarci wadannan ‘yan banga su sace wani Malam Na’awala da Alhaji Ja’o, bayan dauke masu dabbobi.

KU KARANTA: Ana zanga-zanga saboda an yi ram da Jagoran APC a Zamfara

Har ila yau, wannan Lauya ya fadawa Alkali cewa kawo yanzu babu wanda ya san labarin inda wadannan Bayin Allah da aka sace su ke. Lauyan ya roki Kotu ta duba lamarin mutanen biyu.

Tsohon Kwamishinan na jihar Zamfara ya ce bai aikata laifin da ake tuhumarsa ba. Dankande Gamji, ya musanya zargin da ake yi masa, inda ya umarci Lauyansa ya wanke sa a gaban kuliya.

Lauyan da ke kare Jagoran na APC, Bello Umar, ya bukaci Lauyan gwamnati ya ba shi takardar karar. Mai kare gwamnati, ya yi alkawarin zai ba mai kare wanda ake zargi takardun daga baya.

Barista Bello Umar ya roki kotu ta yi watsi da karar da ke gabanta domin ba ta da hurumin shiga shari’ar. Lauyan ya ce an aikata laifuffukan ne a cikin Garuruwan Bakura da kuma Talata Mafara.

Alkali mai shari’a Hadi Sani yace zai duba lamarin domin ganin ko kotunsa ta na da hurumin sauraron shari’ar. Alkalin ya hana beli, ya bukaci a daure wanda ake zargi zuwa 12 ga Disamba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Online view pixel