Taraba: An hallaka Masu Gari da wasu Mutane a Garin Karim Lamido

Taraba: An hallaka Masu Gari da wasu Mutane a Garin Karim Lamido

Masu sarautar gargajiya biyu aka kashe yayin da wasu ‘Yan bindiga su ka aukawa Garin Karim Lamido da ke Jihar Taraba. Jaridar Daily Trust ta rahoto wannan a Ranar 26 ga Nuwamban 2019.

Rahotanni sun bayyana cewa bayan wadannan Sarakuna da aka kashe, an kuma hallaka wani shugaban ‘yan banga da ke Garin na Karim Lamido. ‘Yan bindiga kusan 30 su ka far ma Garin.

Wadanda su ka shaida wannan mugun hari, sun ce ‘yan bindigan sun shiga Kauyukan biyu ne da bindigogi kirar AK47 inda su ka hallaka masu Unguwannin Bilango ta daya da Bilango ta biyu.

Mazauna Yankin sun fadawa ‘yan jarida cewa ‘yan bindigan sun yi wannan ta’adi ne domin ramuwar gayya a game da wasu masu garkuwa da mutane da ‘yan banga su ka kashe a baya.

Jaridar ta ce an bi Sarakunan Kauyen ne har cikin fadarsu, su ka kashe su. An kuma aika shugaban ‘yan bangan da ke aikin sa-kai a yankin lahira tare da wasu na-kusa da manyan kasar.

KU KARANTA: Gwamnan Jihar Borno ya fara shirin karawa Ma'aikata albashi

Har Magatakardun wadannan Sarakuna biyu ba a bar su ba, sai da ‘yan bindigan su ka kashe su. Sarakunan da aka kashe su ne; Garba Dangari, sai kuma Takwaransa Mai martaba Sarki Ali.

Bugu da kari an kuma yi awon-gaba da yara biyar daga tsohuwar kasar Muri, wanda har yanzu ba a san inda su ke ba. Ana zargin cewa ‘yan bindigan sun tsere da su ne zuwa cikin jihar Filato.

Tuni dai an yi jana’izar Marigayi Mai martaba Garba Dangari, da Sarki Ali da sauran Mamatan. An bizne ne su ne da kimanin karfe 12:00 na rana a jiya Talata, 26 ga Watan Nuwamban 2019.

Kawo yanzu an baza Jami’an tsaro a Garin na Karim Lamido. Duk da haka, Kakakin ‘yan sandan jihar Taraba, DSP David Misal ya ce har yanzu ba a cafke wanda su ka yi wannan danyen aiki ba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel