Babu wanda ya san yadda ‘Yan Majalisar Najeriya za su kashe Biliyoyin kudinsu

Babu wanda ya san yadda ‘Yan Majalisar Najeriya za su kashe Biliyoyin kudinsu

Yayin da ake saura kiris a kammala aikin kasafin kudin shekara mai zuwa, Daily Trust ta ce har yanzu babu wanda ya san yadda majalisar tarayya za ta batar da tarin kudin da aka ware mata.

Shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmed Lawan, da Takwaransa na majalisar wakilai, Rt. Hon. Femi Gbajabiamila, sun yi tsit kan abin da ke cikin kasafin kudinsu na Naira biliyan 125.

‘Yan majalisar tarayyan sun ki bada dama a duba diddikin abin da kasafin kudinsu na shekarar badi ya kunsa. Jaridar ta ce bayan ‘yan majalisar, kowa a cikin duhu ya ke a kan wannan.

A cikin ‘yan kwanakin nan, hukumomi da ma’aikatu gwamnatin tarayya sun ta kare kasafin kudinsu na shekara mai zuwa a gaban kwamitocin Sanatoci da ‘yan majalisun wakilan kasar.

Gwamnatin tarayya ta yi kasafin tiriliyan 10.33 a shekarar da za a shiga ta 2020, daga ciki ‘yan majalisar tarayya za su lashe fiye da kashi 1% na daukacin abin da mutanen kasar za su kashe.

KU KARANTA: An kwarewa Sanatoci baya kan yunkurin kakaba hukuncin kisa

Sanatoci 109 da kuma ‘yan majalisa 360 ne za su tashi da biliyan 125 a shekarar 2020. Idan za a yi wa kowa kudin goro, jaridar ta ce kowane ‘dan majalisa zai samu abin da ya haura miliyan 300.

Babu wanda ya ke da ta cewa a kasafin kudin ‘yan majalisa a Najeriya. Haka zalika akwai sauran hukumomin gwamnatin tarayya da ake mika masu kudinsu kai-tsaye daga asusu a duk shekara.

Daga cikin wadannan hukumomi da ma’aikatu masu cin gashin-kan su akwai majalisar NJC ta masu shari’a, hukumar NDDC, UBEC, PCC, NHRC, NEDC, BHCF sai kuma hukumar nan ta INEC.

Biliyoyin da ‘yan majalisar za su batar a badi ya shafi duk albashinsu da na Hadiman da ke taimaka masu, haka akwai kason NILDS. Majalisar dai ta ce za ta fito da komai a fili nan gaba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel