Sanusi ya roki Gwamnatin Tarayya ta girmama yarjejeniyarta da ASUU

Sanusi ya roki Gwamnatin Tarayya ta girmama yarjejeniyarta da ASUU

Mai martaba Sarkin birnin Kano, Muhammadu Sanusi II wanda shi ne shugaban jami’ar tarayyar Benin, UNIBEN, ya yi magana kan sa-in-sar da ake samu tsakanin Malaman jami’a da gwamnati.

Muhammadu Sanusi na II ya nemi gwamnatin tarayyar Najeriya ta cika duk alkawuran da ta yi wa kungiyar ASUU na Malaman jami’ar kasar, wanda a cewarsa wannan zai gyara harkar ilmi.

Sarkin ya yi wannan jawabi ne a wajen taron da jami’ar ta UNIBEN ta shirya domin yaye ‘Dalibanta a karshen makon nan. Wannan shi ne biki na 45 da aka taba shiryawa a makarantar.

Mai martabata ya ce: “Wani abin damuwar da ke faruwa yanzu shi ne ta-ta-bur-zar da ake yi tsakanin gwamnati da kungiyar Malaman jami’a game da tsarin tattalin arzikin gwamnatin.”

Sarkin ya ce: “Shawara ta ita ce ta yi kokarin cika duka alkawarin da ta dauka ga kungiyoyin jami’o’i; ta zama ta bada damar a zauna cikin lalama da kowane bangare wajen daukar mataki.”

KU KARANTA: Wata mata ta zama Likita duk da ba ta ji kuma ba ta gani

Sanusi II ya ce da zarar an yi wannan, za a daina samun yawan yankewar karatun ‘yan makaranta. Sarkin ya na ganin wannan tangarda da ake samu ya na jawo tabarbarewar ilmi.

Bugu da kari, Mai martaba Sarkin na birnin Kano ya yabawa kokarin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ke yi wajen samun damar karatu a jami’o’i ba tare da wata tangarda ba.

A baya an saba ganin Malaman jami’a sun tafi yajin aiki a kasar wanda wannan ya ke jawo ana yaye bara-gurbin ‘dalibai a ganin Sarki Sanusi II. A halin yanzu an samu takaitar wannan lamari.

A jawabin na sa, Sarkin ya jinjinawa yadda shugabannin UNIBEN su ka zabi sabuwar shugaba, Lilian Salami, ya na mai kira ta yi koyi da ‘yaruwar ta mace Grace Alele Williams, da aka taba yi.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel