Sule ba ya goyon-bayan dakatar da Jonathan domin wasu sun yi abin da ya fi na shi muni a PDP

Sule ba ya goyon-bayan dakatar da Jonathan domin wasu sun yi abin da ya fi na shi muni a PDP

Tsohon gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido, ya bayyana cewa ‘yan siyasan sun saba yaudarar jam’iyyar. Tsohon gwamnan ya ce irin wannan abu ba bako ba ne a tafiyar PDP.

Sule Lamido ya yi wannan jawabi ne a lokacin da ya yi hira da Jaridar The Sun a game da zaben sabon gwamnan jihar Bayelsa da aka yi kwanan nan, wanda jam’iyyar PDP ta sha kashi.

Yayin da ya ke magana game da kiran da ake yi na dakatar da Goodluck Jonathan daga jam’iyya, sai ya ce: “Wasu sun yi fiye da abin da Jonathan ya yi… yaudara ita ce tambarin PDP.”

“A wuri na Jonathan ya na cikin kure-kuren da Obasanjo ya tafkawa Najeriya. Ba na ganin cewa ya kamata a hukunta Jonathan a kan abin da ya yi. Sam yin hakan bai da wata ma’ana.”

Tsohon gwamnan na jihar Jigawa ya kara da cewa: “Mutanen da su ke gaba da Jonathan, su ka girmesa, kuma su ke iya yin abin da ya zarce na sa, sun yi abin da ya fi wanda ya yi muni.”

KU KARANTA: Ko a wace Jam’iyya aka tsaida ‘Dan Arewa shi zan zaba a 2023 – Kwande

A game da Jonathan a zaben na Bayelsa, Sule ya ce: “Ya yi koyi ne da manyansa na siyasa da jagororinsa. Sule ya nuna cewa kusan duka ‘yan siyasar APC sun fito ne daga cikin PDP.

“A ra’ayina, idan ka na maganar APC, 80% na ta PDP ne; kun san wannan. Duk wanda ya ke wani abu a majalisa tsakanin 1999 zuwa 2015, ya yi jam’iyyar PDP.” Inji Alhaji Sule Lamido.

Ba nan kadai ya tsaya ba, Sule ya kara da: “Duk wanda ya ke cikin gidan gwamnati a matsayin wani babba a yau, ya yi PDP.” Ya ce, saboda haka yaudara a jinin jam’iyyar PDP ta ke.

Sule Lamido ya ce Jonathan ya yaudari PDP ne saboda gwamnatin tarayya ta taso shi gaba don haka ya saida jiharsa ga jam’iyyar da ta rika bata shi, ta na ci masa mutunci a baya.

“Badakalar Malabo ta yi tasiri a nan. Kuma na fada domin na san abin da ya faru a kan Malabu don har sai da na yi magana da Jonathan. Ya saida jiharsa ne don ya samu ya tsira.”

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Online view pixel