Yaki da ta’addanci: Buhari ya saya ma rundunar Sojojin sama sabbin jirage yaki na zamani 18

Yaki da ta’addanci: Buhari ya saya ma rundunar Sojojin sama sabbin jirage yaki na zamani 18

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya saya ma rundunar Sojin saman Najeriya sabbin jiragen yaki na zamani guda 18 domin kara mata karfi a yakin da take yi da yan ta’adda, wanda a yanzu haka ake tsumayin isowarsu Najeriya.

Babban hafsan sojan sama, Saddique Abubakar ne ya bayyana haka a yayin bude taron samun horo na kwanaki biyu wanda rundunar ta shirya ma jami’anta a kan dabarun sadarwa a babban birnin tarayya Abuja, a ranar Talata.

KU KARANTA: EFCC ta kama kansila da ya yi damfarar naira miliyan 2.3 a Kaduna

Da yake jawabi a yayin bude taron, Saddique, wanda ya samu wakilcin shugaban sashin mulki na rundunar Sojan sama, Kingsley Lar, ya bayyana cewa rundunar ta sayi wadannan jirage 18 ne sakamakon goyon bayan da take samu daga gwamnatin tarayya.

Ya kara da cewa baya ga sabbin jiragen yaki 18 da suke tsumayin isowarsu Najeriya, rundunar ta gyara tsofaffin jiragenta guda 20, wanda a yanzu haka suna aiki, kuma suna bada gudunmuwa wajen yaki da Boko Haram.

Haka zalika yace rundunar ta gudanar da manyan ayyuka sama 900 da suka hada da gina gidaje, ofisoshi, wajen hutawan manyan sojoji, makarantu, azuzuwa, asibitoci da dai sauransu.

“Daga cikin jiragen da muke jiran isowarsu akwai Tucano Jets guda 12, JF-17 Thunder Multi-role guda 3, Augusta 109 Power attack helicopter guda 2 da kuma Agusta 139 utility. Akwai kuma jiragen da muka gyara, wanda a yanzu suna taimaka mana a yaki da ta’addanci.” Inji shi.

Bugu da kari, babban hafsan sojan saman ya bayyana cewa rundunar na sane da muhimmacin mutum a aikin Soja don haka ne ta dauki sabbin kananan Sojoji da hafsoshi da dama, wanda hakan yasa adadin jami’an rundunar sun kusa ninkawa.

Daga karshe kuma yace rundunar ta horas da rukunin sojojinta daban daban a fannoni daban daban da suka hada da bangaren aikin soja na sama da na kasa, a ciki da wajen kasar nan, kamar yadda kamfanin dillancin labarun Najeriya, NAN, ta ruwaito shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel