Matar da ta saci wani karamin yaro za ta yi zama a gidan kurkuku a Ekiti

Matar da ta saci wani karamin yaro za ta yi zama a gidan kurkuku a Ekiti

Kotun majisatare da ke Garin Ado Ekiti a jihar Ekiti ta yanke hukuncin daurin wasu shekaru a gidan yari ga wata Mata mai shekaru 39 da aka kama ta saci karamin jariri mai wata guda.

Wannan Baiwar Allah mai suna Mercy Momoh za ta shafe shekaru uku ne a gidan kaso kamar yadda Alkali mai shari’a Adesoji Adegboye ya yanke hukunci, bayan an kama ta da laifi karara.

Alkalin bai bayyana adereshin wanda aka samu da laifi ba, amma ya tabbatar da cewa za ta yi zaman kaso. Wanda ake tuhuma ta amsa laifinta da kanta, ta na mai rokon Alkali ya yi mata rai.

A Ranar Litinin, 18 ga Watan Nuwamban 2019, jaridar Vanguard ta rahoto mana cewa kotu ta bada damar belin maras gaskiyar a kan kudi N100, 000 a maimakon daurin bayan da ta nemi afuwa.

KU KARANTA: An kama Dalibi saboda ya soki wani 'Dan Majalisa a Kano

Sajen Samson Osobu, wanda shi ne Jami’in ‘dan sandan da ya ke tuhumar wannan Baiwar Allah, ya bayyanawa kuliya Mercy Momoh ta aikata wannan laifi ne a Ranar 20 ga Satumban bana.

Osobu ya ce Momoh ta sace jaririn mai wata daya ne a sakatariyar gwamnatin jihar Ekiti da ke babban birnin jihar. Matar ta sace jaririn ne daga hannun Mahaifiyarsa mai suna Funmi Dada.

Jami’in ‘dan sandan ya fadawa kotu cewa Matar ta yaudari Mahaifiyar jaririn ne da cewa ana rabawa marasa karfi kudi a Sakatariyar jihar, a nan ita kuma Uwar ta bata jaririyarta da wayarta.

Ko da Uwar jaririn ta dawo, sai ta iske babu wannan mata sama ko kasa, haka zalika ta yi gaba da karamin yaronta goyen. Daga nan ta kai kara wajen ‘yan sanda har aka dace aka cafke matar.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Online view pixel