Zaben Bayelsa: Buhari ya taya zababben gwamnan Bayelsa David Lyon murna
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya taya dan takarar gwamna na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a zaben ranar 16 ga watan Nuwamba a jihar Bayelsa, David Lyon, murnar nasarar da ya samu.
Hukumar zabe mai zaman kanta a safiyar ranar Litinin ta kaddamar da Mista Lyon a matsayin wanda ya lashe zabe.
Baturen zabe, Faradey Orumwese, Shugaban jami’ar Benin, ne ya sanar da cewa Mista Lyon ya samu kuri’u 352,552 wajen kayar da Duoye Diri na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) wanda ya samu kuri’u 143,172.
Mista Lyon ya lashe kananan hukumomi shida cikin takwas a jihar. Zaben ya fuskanci rikici a wasu yankunan jihar a cewar masu lura.
Buhari ya yaba na magoya bayan APC da sauran yan Najeriya a jihar wadanda suka sauke nauyin da ya rataya a wuyansu.
Ya yi Allah wadai da rasa rayukan da aka yi sannan ya yi ta’aziyya ga iyalan wadanda abun ya cika da su, cewar kakakinsa Femi Adesina a wani jawabi.
KU KARANTA KUMA: 2019:Jami’in INEC ya ce an ba shi rashawar N50000 a zaben Gwamnan Kogi
Ya ce Buhari ya lura cewa jami’an hukumar zabe da hukumomin tsaro sun yi iya bakin kokarinsu wajen tabbatar zabe na gaskiya.
A baya mun ji cewa tsohon shugaban kasar Najeriya, Goodluck Jonathan ya karbi bakoncin gwamnonin jam’iyyar APC guda biyu a gidansa dake garin Otuoke na jahar Bayelsa a ranar Lahadi, 17 ga watan Nuwamba.
Jaridar The Cables ta ruwaito wadannan gwamnoni na jam’iyyar APC da suka kai ma Jonathan ziyara sun hada da gwamnan jahar Jigawa, Abubakar Badaru da gwamnan jahar Kebbi, Atiku Bagudu, sai kuma hadimin shugaban kasa Muhammadu Buhari, Ita Enang.
Tawagar gwamnonin ta samu kyakkyawar tarba daga tsohon shugaban kasa Jonathan da uwargidarsa Dame Patience Jonathan. Gwamna Badaru da Gwamna Bagudu ne jagororin yakin neman zaben jam’iyyar APC a zaben gwamnan jahar.
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Asali: Legit.ng