Sal Lavallo: Yana da shekara 27 ya ziyarci kowacce kasa a duniya yana neman addinin gaskiya, Allah da ikon sa yanzu dai ya Musulunta

Sal Lavallo: Yana da shekara 27 ya ziyarci kowacce kasa a duniya yana neman addinin gaskiya, Allah da ikon sa yanzu dai ya Musulunta

-Sal Lavallo matashi ne mai shekaru 29 a duniya wanda ya zagaya kasashen duniya kaf don neman addinin gaskiya

- Ya fara neman addinin gaskiya ne tun yana da shekaru 17 a duniya kuma ya hadu da addinai daban-daban

- A kasar Tanzania ne yayi gam da katar inda ya hadu da wani mutum mai hikima da yayi mishi bayanin Musulunci

Addinin Musulunci shine makomar kowanne mutum da ke neman gaskiya. Allah mamallakin kowa da komai kadai ke iya shiryar da wanda ya so.

Wannan labarin wani matashi ne da ya bazama cikin duniya sanin Ubangiji bayan da ya yi zurfi a camfi. Ya je kowacce kasa a duniya a lokacin da ya ke matashi inda daga baya ya karbi addinin gaskiya.

An haifi Sal Lavallo a ranar 11 ga watan Satumba 1990 a cikin addinin kiristanci na mabiya Katolika. Ya kafa tarihi babba na mutum mafi karancin shekaru da ya zagaya duniya baki daya.

Yayi makarantar kiristoci ta shekaru 11. A kullum danginsa na fada mishi cewa, imani nemansa ake yi, kuma babu laifi idan mutum ya samo ilimi mai zurfi fiye da wanda coci ke koyarwa.

A lokacin da ya cika shekaru 17, ya koma rayuwa a Texas tare da wasu iyalai wadanda suka nuna mishi hanyar tsaface-tsaface.

KU KARANTA: Innalillahi: Walkiya ta kashe mutane 27 yayin da da yawa kuma suka jikkata

Ya fara ganin Yesu a matsayin annabi ba Ubangiji ba. Zuciyar shi ta kasa samun natsuwa. A haka ne kuwa ya bazama duniya neman addinin gaskiya.

A watan Fabrairu 2013, ya iso wani kauye a kasar Tanzania. Ya hadu da wani mutum mai hikima kuma ya yi mishi tambayoyi a kan Imani. Sal ya bashi labarin yadda ya fito neman ubangiji. Bayan da mutumin ya gama sauraron shi, ya kira shi cikin addinin Musulunci.

Ya yi bincike a kan Musulunci kuma ya gano abinda zuciyarshi take so. Ya koyi abubuwa da yawa a kan sallah, Annabi da Allah. Ya karba Kalmar shahada a ranar. Ya kuma karbi Musulunci hannu bibbiyu kuma ya gane shine addinin gaskiya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel