Dadin kowa: Kamaye ya bayyana dalilin da yasa yake fitowa talaka tilis

Dadin kowa: Kamaye ya bayyana dalilin da yasa yake fitowa talaka tilis

Shahararrun jaruman nan masu fitowa a fitaccen wasan kwaikwayon nan na arewacin Najeriya wanda ake nunawa a tashar "Arewa24", mai suna "Dadin Kowa", Adama da Kamaye, sun ce ba karamin farin jini wasan kwaikwayon ya jawo musu ba a wajen mutane.

Dan Azumi Baba, wanda aka fi sani da Kamaye a shirin, mai gidan Adama, ya ce yana fitowa a shirin a matsayin matalauci ne saboda haka bukatar daraktan shirin ta so. Hakan kuwa yasa mutane ke masa kallon so da tausayi.

Hakazalika, kamaye ya ce, rawar da yake takawa a shirin ta bayyana shi a duniya tare da daukakasa. Ya kara da cewa, yana zama tauraro a duk inda ya shiga.

Kamaye tun asali, marubuci ne kuma darakta ne a masana'antar Kannywood. A cikin fina-finansa akwai: Babban gari, Duhun daji, Juda, Dandazo da sauransu. A fina-finan kuwa an san sunan Dan Azumi Baba.

DUBA WANNAN: Yadda dalibin jami'ar Legas ya harbi wani mutum a mazakuta

Ita kuwa Hajiya Zahra'u Sale, wacce ke fitowa a matsayin Adama kuma matar Kamaye, ta ce rawar da take takawa a shirin na masifaffiya kuma mara tausayin miji, yasa wasu ke mata kallon haka a zahiri. Amma kuma tace, akwai wadanda basa nuna mata kyama. Adama ta kara da cewa, tana fitowa ne a halin da masu kallo ke ganinta ciki saboda isar da sako tare da manufar wasan kwaikwayon.

Adama ta ce ta kan samu sakonnin zagi da cin mutunci daga wadanda basu fahimceta ba, duk da kuwa akwai masu fahimta da suka san wasan kwaikwayo ne.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel