Hazikan lauyoyin da suka zama SAN da kananan shekaru a Najeriya

Hazikan lauyoyin da suka zama SAN da kananan shekaru a Najeriya

Zama babban lauya a Najeriya ba abun wasa ba ne. Ana fara kiran lauya 'SAN' ne a kalla idan yayi shekaru 10 yana aiki kuma an tabbatar da kwarewarsa. Tun da aka fara bada matsayin a shekarar 1975, lauyoyi 545 ne suka samu matsayin a Najeriya.

Ana bada matsayin ne kamar yadda dokar aikin ta 207 ta tanadar kuma kwamitin lauyoyin wanda ke samun jagorancin shugaban lauyoyin Najeriya ke shugabanta ke badawa.

Lokacin da aka fara bada matsayin, a ranar 3 ga watan Afirilu, 1975, marigayi Frederick Rotimi Alade Williams da Dr. Nabo Graham Douglas ne aka fara karramawa da matsayin. Tun daga nan, sama da lauyoyi 500 aka ba matsayin. Wasu na da rai inda wasu suka rigamu gidan gaskiya.

Wasu daga cikinsu sun samu sa'ar samun wannan matsayi a lokacin da suke da kananan shekaru sakamakon kwazonsu da jajircewarsu. Ga kadan daga cikin lauyoyin da suka samu wannan matsayin da kananan shekaru:

DUBA WANNAN: Korar hadiman Osinbajo 35: Kakakin mataimakin shugaban kasa ya karyata batun

1. Babatunde Raji Fashola

Tsohon gwamnan jihar Legas kuma ministan gidaje da aiyuka a yanzu. Ya zama babban lauyan Najeriya ne lokacin da yake da shekaru 41 a shekarar 2004 bayan da yayi aiki sama da na shekaru goma.

2. Kehinde Olamide Ogunwumiju

An karrama shi da wannan matsayi ne yana da shekaru 36 a duniya. Ya samu matsayin ne a ranar 18 ga watan Satumba, 2017 bayan da yayi aikin shekaru 12.

3. Alex Izinyon

Izinyon ya samu wannan matsayi ne a 1991 lokacin da yake da shekaru 41 a duniya.

4. Ahmed Raji

Ahmed Raji babban lauya ne a Najeriya kuma ya samu wannan matsayin ne lokacin da yake da shekaru 49 a duniya. Yana da gogewar aiki don yayi kwamishinan zabe a jihohi daban-daban na fadin kasar nan.

5. Joseph Bodunrin Daudu

Joseph Daudu ya samu wannan matsayin ne a shekarar 1995 lokacin yana da shekaru 36 kacal a duniya.

6.Yusuf Olaolu Ali

Yusuf Olaolu Ali lauyan Najeriya ne gogagge kuma masani a fannin doka. Ya samu matsayin babban lauyan Najeriya ne a shekarar 1997.

7. Ebun-Olu Adegboruwa

Ya fara zirga-zirga ne a kasa mai habaka ta Najeriya. Kamar yadda yace, an kamashi, an koreshi kuma na hanshi hakkinshi amma hakan bai zamo shinge tsakaninsa da burinsa ba. Malamin harshen turanci ne a jami'o'in Najeriya. Ya samu matsayin ne a watan Satumba 2019.

8. Muyiwa Atoyebi

Atoyebi ne mafi karantar shekaru a tarihin lauyoyin da suka samu wannan matsayi. Ya samu ne yana da shekaru 34 a duniya a shekarar 2019. Yana daga cikin lauyoyi 38 da aka ba matsayin a wannan shekarar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel