A rika gano masu garkuwa da mutane ta lambar salularsu – Sanatoci ga Gwamnati

A rika gano masu garkuwa da mutane ta lambar salularsu – Sanatoci ga Gwamnati

Majalisar dattawan Najeriya ta bukaci Ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Isa Ali Pantami, ya gano hanyar da za a rika gano masu garkuwa da mutane ta lambobin wayoyinsu.

Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan ne ya yi wannan kira da kansa a lokacin da aka bude zauren majalisar a jiya Laraba, 6 ga Watan Nuwamban 2019, kamar yadda rahoto ya zo mana.

Sanatocin sun kuma nemi Mai ba shugaban kasa shawara kan harkar tsaro, Janar Babagana Moguno mai ritaya da ya fara shirin sayo jirage masu shawagi ba tare da matuki ba a fadin kasar.

Majalisar ta na gani wadannan dabaru za su taimaka wajen rage matsalar garkuwa da mutane da ake yi a Najeriya. Lawan ya yi kira a samu layin da zai rika hada jama’a da duk jami’an tsaro.

KU KARANTA: Ministan sadarwa, Pantami, ya haramtawa NIPOST karbar kudi

“Dole mu samu hanyar bin kadin masu garkuwa da mutane ta hanyar wayoyin salulansu. Ya kamata ace Najeriya ta kafa wani akwatin waya na kiran gaggawa makonni biyu da su ka wuce.”

Lawan ya kuma ce: “Mun yi kokarin hada kan gaba daya jami’an tsaro su samu lambar layi guda a maimakon a samu akwatin waya dabam-dabam. Mu na so a kafa wani layin bada agaji a ko ina.”

“A cikin wata guda da ya wuce na yi ta ganawa da jami’an tsaro da Ministocin sadarwa da birnin tarayya. Abin da mu ke yi shi ne kawo hanyoyin yakar garkuwa da mutane da matsalar tsaro.

Majalisar dattawan ta na so gwamnatin tarayya ta kaddamar da layi na musamman wanda zai sa a iya tuntubar jami’an tsaro a lokacin daaka shiga cikin halin ha’ula’i a ko ina a cikin Najeriya.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel