Sale Dandashire ya zama Gwarzon Likitocin ABU Zariya na 2019

Sale Dandashire ya zama Gwarzon Likitocin ABU Zariya na 2019

- Sale Dandashire ne ya zama Gwarzon Likitocin ABU Zariya a bana

- Matashin ya lashe kyaututtuka har 13 shi kadai a bikin yaye Likitoci

- Dandashire ya fito ne daga cikin jihar Katsina a Arewacin Najeriya

Mun samu labarin wani Matashi da ya kammala karatun ilmin Likita a fitacciyar Jami’ar nan ta Ahmadu Bello da ke Zariya. Wannan Bawan Allah dai ya kere sa’a a shekarar nan.

Dakta Sale Muhammed Dandashire, shi ne ya zama Gwarzon ‘Daliban Likitoci na shekara ta 2019 da jami’ar ABU Zariya ta yaye. Sale Dandashire ya tashi ne da kyaututtuka har 13.

Kamar yadda mu ka samu labari, Dr. Sale Dandashire ainihinsa mutumin Garin Kankara ne da ke cikin jihar Katsina. Jama’a da-dama dai sun jinjinawa irin hazakar wannan Matashi.

KU KARANTA: Najeriya za ta shigo da wasu Likitoci daga kasashen waje

Dandashire shi ne ya zo na daya a kwas da-dama, daga ciki akwai fannin harkar jini, da ilmin cikin jikin mutum da na cututtuka. Hakazalika binciken Dandashire shi ne ya ciri tuta a 2019.

Mun samu wannan labari ne daga wani Takwaransa Likita mai suna Dr. Abdulrahman A Shehu. Shi ma dai Dr. A Shehu ya kammala karatunsa ne daga wannan jami’a a 'yan shekarun baya.

A hoton da ya rika yawo a makon jiya da aka yi bikin yaye wadannan ‘Dalibai daga jami’ar ABU Zariya da ke Kaduna, an ga Dr. Dandashire tare da wadannan kyaututtuka na sa rututu.

Matashin Likitan shi ne ya zo na daya a cikin sa’anninsa a bangaren fida. A shekarar da ta wuce wata Budurwa mai suna A'eesha Humayrah Abaji ce ta lashe irin wadannan kyaututtuka.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel