Mutuwar mai laifi: Jarumin dan sanda Abba Kyari ya shiga tsaka mai wuya

Mutuwar mai laifi: Jarumin dan sanda Abba Kyari ya shiga tsaka mai wuya

A ranar Talata ne wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Jos, jihar Filato, ta umarci babban sifeton rundunar 'yan sanda da jarumin dan sanda Abba Kyari, mai mukamin mataimakin kwamishina, wanda kuma ke jagorantar wata runduna ta musamman mai lakabin IRT (Intelligence Response Team), da su gabatar da wani mai laifi a gabanta, da rai ko a mace.

Alkaliyar kotun, Jastis Dorcas Agishi, ta bayar da wanna umarnin ne bayan D. G. Dashe, lauyan mutumin da aka kama mai suna Mista Nanpon Sambo ya shigar da korafi a gabanta, inda ya yi zarhin cewa mutumin da yake kare wa ya mutu a hannun rundunar 'yan sanda a Abuja.

Alkaliyar kotun ta bawa manyan jami'an 'yan sandan sati biyu domin su fito da mai laifin ko kuma su fuskanci fushin doka.

Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya rawaito cewa Dashe ya fara rubuta takardar koke zuwa kotun a ranar 25 ga watan Satumba domin neman a tilasta IGP da Kyari su gabatar da Sambo a gaban kotu bayan kama shi da rundunar 'yan sanda ta yi bisa zarginsa da mallakar bindigu ba bisa ka'ida ba.

"Idan ma rundunar 'yan sanda ta binne mai laifin bayan ya mutu, ina umartar ta hako shi daga kabari tare da kai gawarsa asibitin koyar wa na jami'ar Jos domin gudanar da binciken masana a kansa," a cewar ta.

Agishi ta yi gargadin cewa za ta dauki mataki mai tsanani matukar sati biyu suka cika ba tare da IGP da Kyari sun yi biyayya ga umarnin da ta bayar ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng