Duk wanda ya ke da hujjar Bola Tinubu ya saci kudi ya kawo – Jam’iyyar APC

Duk wanda ya ke da hujjar Bola Tinubu ya saci kudi ya kawo – Jam’iyyar APC

Mun ji cewa Jam’iyyar APC ta maida martani a game da korafin jagoranta, Asiwaju Bola Tinubu, da aka kai gaban hukumar EFCC bisa zargin cewa an ga motocin kudi a gidansa lokacin zabe.

A Ranar Oktoba 25 ne Deji Adeyanju da wasu mutum biyu; Ariyo Dare Atoye da Adebayo Raphael su ka kai korafi wajen EFCC na cewa an hangi manyan motocin kudi a cikin gidan ‘dan siyasar.

Daily Trust ta ce wannan ya jawo dar-dar a cikin jam’iyyar ta APC inda ake zura idanu domin ganin ko jami’an hukumar kasar za ta nemi ta taso Jagoran jam’iyyar a gaba ko kuwa ya za a kare.

A wata hira da ‘yan jaridar su ka yi da babban jigon APC a jihar Legas, yayi watsi da wannan korafi da aka kai gaban hukumar mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon-kasa.

KU KARANTA: An fara dakile Bola Tinubu a APC - Tsohon Gwamna

Kakakin Jam’iyyar APC mai mulki a Legas, Hon. Abiodun Salami, ya kalubalanci masu jefa wannan zargi inda ya fadawa Manema labarai cewa: “Su kawo hujjar cewa Tinubu ya saci kudi.”

“Mutumin nan zaman kansa yake yi kuma ba ya cikin gwamnati na tsawon shekaru goma sha biyu. Idan ya ga dama ya kashe kudinsa a kan jam’iyya, ta ya aka yi wannan ya zama matsala?”

Salami wanda ke magana da yawun APC, ya nemi duk wanda yake cewa tsohon gwamnan na Legas ya wawuri dukiyar gwamnati ya bankado hujjojin da ke nuna kudi sun bace a wani wuri.

Hukumar EFCC dai ta tabbatar da karbar korafin Kwamred Deji Adeyanju inda aka yi mata wasu jerin tambayoyi da ke bukatar amsa. Kawo yanzu dai ba a ji wani mataki da hukumar ta dauka ba.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel