Hukumar EFCC ta karbi korafi a game da wasu zargi kan Tinubu a zaben 2019

Hukumar EFCC ta karbi korafi a game da wasu zargi kan Tinubu a zaben 2019

Hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa a Najeriya ta bayyana cewa ta samu korafi da aka kawo a game da tsohon gwamnan jihar Legas, Bola Ahmed Tinubu.

Ana zargin cewa wata motar kudi ta shiga gidan Jigon na jam’iyyar APC mai mulki ana gaf da zaben shugaban kasa a farkon bana. Ana so hukumar ta duba silar wadannan makudan kudi.

Korafin da ke gaban EFCC ya ce: “Hukumar za ta iya tuna cewa labarai sun karada ko ina cewa an ga wata mota cike da makudan kudi za ta shiga cikin gidan tsohon gwamnan jihar Legas…”

Aka cigaba da cewa: “…Bola Ahmed Tinubu a Ranar jajibirin zabe. Shi kansa tsohon gwamnan na Legas ya tabbatar da wannan a lokacin da yake amsa tambayoyin da ‘yan jarida su ka yi masa.”

KU KARANTA: Hukumar CCB ba za ta bayyanawa Duniya sirrin dukiyar Buhari ba

“Ya kamata ku sani cewa sashe na 7 na dokar da ta kafa EFCC ta bada ikon binciken dukiyar duk wani mutumi da ake da shakku bisa ga irin kashe kudinsa tare da la’akari da irin samunsa.”

“A iyaka bakin ilminmu, Bola Ahmed Tinubu gama-garin mutum ne wanda bai kamata ace an gani da tawagar motoci dankare da kudi ba.” Mai korafin ya cigaba da jefawa hukumar tambayoyi.

“Tambayoyin da ke bukatar amsa su ne: Mai motocin kudi su ke yi a gidan of Asiwaju Bola Ahmed Tinubu? Wa ke dauke da abin da ke cikin wadannan motoci, wanda ake tunanin cewa kudi ne?”

“Shin hukumar ta binciki inda aka samo wadannan kudi a matsayin ta na hukumar da ke da wannan alhaki. Ko gidan Bola Tinubu ya zama banki ne inda motoci ke kai makudan kudi.?”

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel