Hajj: Farashin shiga Saudiyya ya tashi daga $93 (N30, 000) zuwa $530 (N180, 000)
Wani rahoto da mu ka samu daga Jaridar News18 ta Indiya tace kasar Saudi Arabiya ta kara kudin takardun biza, sannan kuma an yi sama da farashin aikin Hajji ga masu shirin yin mai-mai.
Kamar yadda mu ka ji, za a rika karbar $533 ga masu bukatar bizan shiga guda zuwa kasa mai tsarkin. A baya abin da ake biya bai wuce $93 ba. Hakan na nufin an ribanya kudin sau shida.
Masu neman iznin shiga kasar Saudi na tsawon watanni shida, za su biya $800. Haka zalika a wannan sabon tsari da aka kawo yanzu, duk wanda zai shafe shekara guda a kasar zai biya $1333.
Jaridar tace wannan mataki da aka dauka bai yi wa jama’a da-dama dadi ba. Musulmai na yawan zuwa kasar Saudi domin sauke faralin aikin Hajji ko kuma ziyarar Umrah lokacin bayan lokaci.
KU KARANTA: Shugaban kasa Buhari ya dawo kan Malamai masu lalata da ‘Dalibai
Ma’aikatar tattalin arzikin kasar ce ta bada shawarar a kara kudin biza. Wannan doka ya fara aiki tun Ranar 2 ga Watan Oktoba. Wannan ya zo daidai da lokacin sabuwar shekarar Hijirar Islama.
Saudiyya mai arzikin man fetur ta gamu da tangarda ne bayan da farashin man fetur ya karye a kasuwar Duniya. Dogon yakin da kasar ta ke yi da Yemen ya kuma taba tattalin arzikin kasar.
Wannan matsala da aka samu na fannin tattali ne ya sa gwamnatin Saudi ta sanar da cewa za ta ragewa ma’aikatanta albashi. A tarihi wannan ne karon farko da aka datse albashin ma'aikata.
Kasashe irin su Maroko za su yi baram-baram daina zuwa Hajji idan ba a rage wannan kudi ba. Rahotanni sun ce Turkiya, da Masar da Najeriya duk sun nuna cewa ba su yi na’am da karin ba.
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi
https://fb.gg/play/ramadan_ramadan
Asali: Legit.ng