Bazan iya soyayya da budurwar da take daukar albashin kasa da N250,000 ba a wata - In ji wani saurayi

Bazan iya soyayya da budurwar da take daukar albashin kasa da N250,000 ba a wata - In ji wani saurayi

- Wani saurayi mai amfani da shafin sadarwa na Twitter ya bayyana cewa ba zai taba yin soyayya da budurwar da take daukar albashi kasa da N250,000 ba a wata

- A wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Twitter, ya ce shi mutum ne mai tattali saboda haka yana neman mace mai irin halin shi

- Rubutun da Buchi ya wallafa ya jawo kace-nace matuka, inda kowa ke fadar albarkacin bakin sa

Wani mai amfani da shafin sadarwa na Twitter mai suna Solomon Buchi ya bayyana cewa ba zai taba iya soyayya da budurwar da take daukar albashi kasa da dubu dari biyu da hamsin ba a wata.

Wannan rubutu da Buchi ya wallafa ya jawo kace nace matuka a shafukan sada zumunta, inda har wasu matan suka kira shi da mai auren jari, wanda yake so yayi arziki ta hanyar matar shi.

Buchi ya ce idan har mace za ta kira namiji da irin wannan sunan, ita kuma mai ya kamata a kirata da shi kenan?

KU KARANTA: Asirin wasu jami'an hukumar FRSC ya tonu, bayan an gawo gawar wani mutumi da suka kashe suka binne gawar shi

"Idan har za'ayi la'akari ta bangaren soyayya, kudi yana taka muhimmiyar rawa a harkar soyayya, kuma rashin kudi na iya kawo karshen soyayya ko aure. Saboda haka kada kowa yaga laifin mace ko namiji da yake neman abokin rayuwa mai kudi, haka kuma bai kamata ace dole sai an kayyadewa mutum yawan kudin da zai dauka ba kafin ayi soyayya da shi," in ji shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel