Tinubu: Ilmi mai nagarta ne kurum maganin talauci da jahilci

Tinubu: Ilmi mai nagarta ne kurum maganin talauci da jahilci

Jagoran jam’iyyar APC mai mulki, Asiwaju Bola Tinubu, yace ilmi mai nagarta babban makami ne wajen yaki da talauci da jahilci a Najeriya. Tinbubu ya bayyana wannan ne a karshen makon jiya.

A lokacin da Asiwaju Bola Ahmed Tinubu yake jawabi wajen yaye ‘Daliban jami’ar Afe Babalola da ke Garin Ado Ekiti, yace ilmi ne hasken da zai iya kawowa duk wata al’umma cigaba da nasara.

Jami’ar ta Afe Babalola da aka fi sani da ABUAD ta yaye ‘Dalibanta na bakwai kenan tun kafuwarta. Wannan biki ya zo a daidai lokacin da jami’ar jihar ta Ekiti ta shekara goma a Duniya.

Kamar yadda mu ka samu labari, an samu akalla mutane 99 da su ka kammala karatu da matakin farko na Digiri. Daga cikinsu akwai yara hudu da gwamnatin tarayya ta dauki nauyin karatunsau.

KU KARANTA: Haifaffen Jihar Legas ya shiga sahun manyan Masanan tarihi a Turai

Jawabin yace: “Ilmi ne kurum abin da zai haske al’umma daga duhun jahilci. Da haske ne kadai za mu iya ganin hanyar da mu ke tafiya a kai domin kai w aga nasara a matsayin al’ummar kasa.”

“Ilmantar da jama’a kamar nema masu madafa ne nan gaba. Don haka ina farin cikin kasancewa tare da ku a nan domin wannan jami’a ta na cikin Taurarin da ke haska harkar ilmin kasar mu.”

Tinubu ya kanbama jami’ar inda ya ce ta zama turbar cigaban Najeriya. Yaranmu masu tasowa su na bukatar ilmi mai nagarta da zai sa su kai ga nasara. Wannan ne kuma zai kawo cigaba a kasa.

Daily Trust ta rahoto cewa an karrama Sarkin Musulmi Muhammadu Sa’ad Abubakar, Sarkin Onitsha, Igwe Nnaemeka Achebe da wani ‘dan kasuwa Anthony Adegbulugbe da Digiri a bikin.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel