David Olusoga ya zama Shehin Malamin tarihi a Jami’ar Manchester a UK

David Olusoga ya zama Shehin Malamin tarihi a Jami’ar Manchester a UK

Tauraruwar David Olusoga ce ta ke cigaba da haskawa inda yanzu ya zama Farfesa a jami’ar Garin Manchester da ke cikin kasar Birtaniya bayan irin kokarin da ya yi a fannin shirye-shiryen tarihi.

David Olusoga wanda aka haifa kusan shekaru 50 da su ka wuce a Legas da ke Kudancin Najeriya ya yi kaurin suna ne wajen ilmin tarihi, harkar yada labarai da kuma shirya wasan kwaikwayo.

Mahaifin wannan Shehin Malami mutumin Najeriya ne yayin da Mahaifiyarsa kuma ta fito daga Birtaniya. Tun ya na yaro Olusoga ya dawo Ingila inda ya tare a Unguwar nan ta Newcastle.

Iyalin Olusoga sun tsere daga Newcastle bayan da aka rika addabarsu da munanan hare-hare. A haka wannan Bawan Allah ya tafi Jami’ar Liverpool inda ya karancin ilmin tarihin cinikin Bayi.

Babban Masanin mai shekaru 49 da haihuwa ya gabatar da shirye-shirye masu ilmantarwa iri-iri game da tarihi. Olusoga ya yi aiki ne na tsawon shekara da shekaru a BBC kafin Duniya ta san shi.

KU KARANTA: Bakar Attajira Oprah ta sayawa wani Saurayi wayar zamani

Haifaffen ‘Dan Najeriyar ya rika aiki ne a bayan fage kafin ya samu damar shigowa cikin shirye-shirye kai tsaye inda a 2014 ya fito da wani shirin da ya tsara a game da yakin Duniya na biyu.

Bayan tarihin yakin Duniya, Masanin ya kuma yi wani shiri a BBC a game da labarin cinikin bayi da Turawan Ingila su ka yi. Olusoga ya dai fito da shirye-shirye iri-iri da su ka shafi fannin tarihi.

Kwazon Olusoga ta sa aka karrama shi da lambar girma na OBE a Ingila. Daga baya kuma jami’ar da yake aiki ta Manchester ta kara masa matsayi zuwa Farfesa a bangaren tarihin al’umma.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel