Zaben Bayelsa: Oshiomhole zai kawo Sojoji saboda ayi murdiya - PDP
Mun ji cewa jam’iyyar PDP ta reshen jihar Bayelsa ta yi tir da abin da ta kira karyayyakin banza daga bakin shugaban jam’iyyar APC na kasa, Adams Oshiomhole na cewa ta na tara makamai.
Jam’iyyar PDP mai mulki a jihar Bayelsa ta musanya zargin da APC ta ke yi na cewa ta adana makaman da za ayi amfani da su wajen zaben sabon gwamnan jihar da za ayi a Watan Nuwamba.
Mista Moses Cleopas yace asali ma dai APC ce ta ke wani yunkuri na shigo da Sojoji domin a murde zaben gwamnan da za ayi a Bayelsa. Cleopas ya ce ba za kuma su yarda da wannna ba.
Jam’iyyar PDP ta bayyana cewa APC ta yi amfani da Dakarun Sojoji wajen murde zaben baya da aka yi na ‘yan majalisa inda har aka kashe wasu Jiga-jigan gwamnati da jam’iyyar PDP a jihar.
KU KARANTA: Gwamnan Bayelsa ya sa-labule da Shugaban kasa Buhari
“Abin ya yi ban-ba-ra-kwai ace shugaban APC da Mataimakin Sakatarensa na yada labarai, Yekini Nabena, su fito su na zargin PDP da ajiye makamai, yayin da APC ce aka sani da rigima a Bayelsa.”
“Mutanen Bayelsa da ‘Yan Najeriya sun san APC jam’iyyar Tsageru ce da ‘yan kungiyar asiri, masu yawan tada rikici. Kokarin sace DCP Kola Okunola da su ka yi a zaben 2019 ya tabbatar da haka.”
Jagoran na PDP a jawabin na sa ya zargi APC da kashe Mai daukar hoton gidan gwamna, Reginald Dei da kuma wani Jigon PDP a Oweikorogham, inda yace wannan duk aikin APC ne.
Shugaban PDP na Bayelsa, Moses Cleopas, shi ne ya fitar da wannan jawabi a madadin jam’iyyara Ranar Lahadi 20 ga Oktoba, 2019 kamar yadda mu ka samu labari daga Jaridar Daily Trust.
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi
https://fb.gg/play/ramadan_ramadan
Asali: Legit.ng