Cigiya: Ana neman wasu Yara Aminatu, Maryam da Khadijah a Jalingo
Mun samu labari cewa ‘Ya ‘yan wani mutumi sun bace daga lokacin da su ka bar gida zuwa Makaranta. Har yanzu dai babu wanda ya sake jin labarinsu.
Wadannan yara mata kanana masu tasowa; Aminatu, Maryam da kuma Khadija sun bar gidansu ne a cikin Keke Napep amma har yanzu ba su dawo gida ba.
Mahaifin wannan yara Alhaji Manu Getdown ya fito ya neman jama’a su taimaka masa wajen cigiyar wadannan yara na sa da aka rasa sawun sun har yau.
Manu Getdown ma’aikacin gwamnati ne wanda yake aiki a Kwalejin harkar gona da ke babban birnin Jalingo da ke jihar Taraba kuma Mazaunin yankin.
KU KARANTA: Kotu ta ce a ba tsohon Jami’in Sojan da aka sallama 2012 Miliyan 10
Wani Bawan Allah mai suna Nasir Abdulkarim, shi ne wanda ya bada wannan sanarwa a shafinsa na Facebook tun Ranar 11 ga Watan Oktoban nan na 2019.
Yanzu haka dai ana kira ga jama’a Mazaunan babban birnin jihar Taraba na Jalingo da su taimaka da duk wani labari da su ka samu a game da ‘Yan matan.
Bayan wannan rahoto mun fara samun kishin-kishin din cewa an samu ganin wadannan yara kwanaki. Wani mai bibiyar shafin mu ya sanar da mu hakan.
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi
https://fb.gg/play/ramadan_ramadan
Asali: Legit.ng