Tamu ta samu: Majalisar Ɗinkin Duniya za ta karrama wata 'yar sandan Nigeria

Tamu ta samu: Majalisar Ɗinkin Duniya za ta karrama wata 'yar sandan Nigeria

- Majalisar Ɗinkin Duniya za ta karrama babbar sufuritanda Catherine Ekwutosi ta rundunar 'yan sandan Nigeria

- MDD ta na karrama jami'an 'yan sanda mata a kowacce shekara, daga cikin wadanda ta tura aikin kwantar da tarzoma a kasashe daban daban

- Majalisar Ɗinkin Duniya ta jinjinawa Ugorji akan kwarewa a aikinta, in da kawo raguwar ta'addanci a a kasar Mali

Majalisar Ɗinkin Duniya ta zabi babbar sufuritanda Catherine Ekwutosi ta rundunar 'yan sandan Nigeria a matsayin daya daga cikin wadanda za ta karrama a shekarar 2020.

MDD ta na karrama jami'an 'yan sanda mata a kowacce shekara, daga cikin wadanda ta tura aikin kwantar da tarzoma a kasashe daban daban.

KARANTA WANNAN: Tankar man fetur ta kama da wuta a gaban ofishin gwamnan jihar Ogun

Tamu ta samu: Majalisar Ɗinkin Duniya za ta karrama wata 'yar sandan Nigeria
Tamu ta samu: Majalisar Ɗinkin Duniya za ta karrama wata 'yar sandan Nigeria - www.thepledge.ng
Asali: UGC

Jaridar The Punch ta ruwaito cewa, a halin yanzu, Ugorji na kasar Mali inda ta ke aikin kwantar da tarzoma karkashin inuwar Majalisar Ɗinkin Duniya.

Majalisar ta sanar da sunan 'yar sandar a cikin wata sanarwa da ta fitar a shafinta na Nigeria.

Rahotanni sun bayyana cewa, akalla 'yan sanda mata na MDD guda 1,300 ne aka tura aikin wanzar da zaman lafiyar, kuma 21 daga cikinsu ne kawai za a karrama.

Sanarwa mai taken, 'Majalisar Ɗinkin Duniya za ta karrama 'yar sandar Nigeria bisa namijin kokarinta a aikin wanzar da zaman lafiya.'

KARANTA WANNAN: Kotu ta hana EFCC takardar izinin cafke Diezani Alison-Madueke

Sanarwar, wacce ta ruwaito babban sakataren sashen wanzar da zaman lafiya na MDD, Mr Jean-Pierre Lacroix, ta ce "Kokari da kalaman Ugorji ya sa MDD za ta bata wannan lambar yabon."

Ta kara da ce, "Babbar Sifeta, Doreen Malambo 'yar kasar Zambia ce ta lashe kambun wannan shekarar a kwantar da tarzoma a Kudancin Sudan, kuma Mr Lacroix ne zai ba ta kambun.

"Za a yi bukin karrama jami'an 'yan sandan ne ta yanar gizo, a ranar Talata, 3 ga watan Nuwamba 2020.

"Sufuritanda Rebecca Nnanga ta kasar Kamaru, da ke aikin kwantar da tarzoma a Jamhuriyyar Afrika ta tsakiya, za ta samu lambar yabo irinta 'yar sandar Nigeria.

"A shekarar 2011 ne MDD ta kirkiri shirin karrama jami'ai mata da ke aikin kwantar da tarzoma karkashin majalisar, domin kara masu kwarin guiwa da karramasu a idon duniya."

A yayin da majalisar ke taya Ugorji murna, mai bada shawara kan 'yan sanda na MDD, Mr Luis Carrilho, ya ce "Hakika Ugorji ta nuna kwarewa a aikinta, ta kawo raguwar ta'addanci a Mali."

A wani labarin, DPO na ofishin 'yan sanda da ke Kubwa, Abdullahi Bello, a ranar Talata ya ce wasu bata gari da suka je yashe sansanin NYSC na Kubwa, sun so caccaka masa wuka yana a bakin aiki.

Mr Bello, wanda bayyana hakan a wata tattauna da kamfanin dillancin labarai na kasa NAN, ya ce sai da shi da mutanensa suka koma gefe, don gudun farmaki daga bata garin.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel