An zabi Abubakar Fulata Shugaban ‘Yan Majalisar Afrika ta Yamma

An zabi Abubakar Fulata Shugaban ‘Yan Majalisar Afrika ta Yamma

‘Dan majalisar wakilan tarayyar Najeriya ne aka zaba a matsayin shugaban zauren IPU na majalisun kasashen Afrika ta yamma. Abubakar Fulata shi ne wanda ya lashe wannan zabe jiya.

Honarabul Abubakar Fulata mai wakiltar Birniwa/Guri/da shiyyar Kiri-Kasamma ya yi nasarar lashe kujerar IPU ne bayan wani zama da ‘yan majalisun Nahiyar su ka yi a can kasar Sabiya.

An sanar da wannan karin matsayi da ‘dan majalisar na jihar Jigawa ya samu ne a Ranar 13 ga Watan Oktoba. Majalisar wakilan tarayyar ta sanar da wannan a shafinta na sadarwa na Tuwita.

A jawabin Abubakar Fulata jim kadan bayan ya samu nasara, ya godewa Kakakinsa watau Rt. Hon. Femi Gbajabiamila, da Tawagar Najeriya ta Ahmed Idris Wase da Zakari Ya'u Galadima.

KU KARANTA: Wata kasa a Afrika ta shiga sahun masu rage albashin ‘Yan Majalisa

Honarabul Fulata ya lashe wannan zabe ne cikin ruwan sanyi a matsayin shugaban majalisun kasashen Afrika ta Yamma. Ba a samu wani ‘dan majalisa da ya yi takara da ‘dan Najeriyar ba.

Shugaban majalisar wakilan Najeriyar, Femi Gbajabiamila ya karbi wannan godiya ta musamman da Abokin aikin na sa ya yi masa tare da wasu manyan ‘yan majalisar kasar a jawabin godiyarsa.

Ga abin da mai wakiltar Mazabar Birniwa da Guri da Mazabar Kiri-Kasammana na jihar Jigawan ya ke fada kamar yadda majalisar wakilai ta tsakuro jawabin na sa a Ranar Lahadin da ta wuce.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng