Kwankwaso ya hadu da Tinubu da Fayemi a wajen daurin aure da bikin Shagaya a Legas

Kwankwaso ya hadu da Tinubu da Fayemi a wajen daurin aure da bikin Shagaya a Legas

A cikin karshen makon nan ne Bola Shagaya ta cika shekaru 60 a Duniya. Fitattun ‘Yan siyasa su na cikin wadanda su ka halarci bikin taya ta murnar ganin wadannan shekaru a ban kasa.

Daga cikin wadanda su ka halarci bikin da aka shirya domin taya Attajirar murna akwai tsohon gwamnan jihar Kano kuma babban ‘dan siyasar hamayya a Najeriya, Rabiu Musa Kwankwaso.

Hon. Abubakar Nuhu Danburam ya na cikin wadanda su ka yi wa Jagoran na Kwankwasiyya rakiya wajen wannan walima da aka shirya a dakin taron otel dinnan na Eko da ke Garin Legas.

Kamar yadda mu ka samu labari, Sanata Rabiu Kwankwaso ya ci karo da Jigon jam’iyyar APC nai mulki a Najeriya watau Asiwaju Bola Tinubu a wannan biki da aka shirya a Victoria Island.

KU KARANTA: Dadi har kumatu bayan Aisha Buhari ta dawo Najeriya

Kwankwaso ya hadu da Tinubu da Fayemi a wajen daurin aure da bikin Shagaya
Kwankwaso rungume da Gwamnan Ekiti a Legas
Asali: Twitter

Tsohon Sanatan na tsakiyar Kano, Rabiu Kwankwaso, ya kuma samu damar haduwa da gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi a wajen. An ga Tsohon Ministan ma’adanan ya rungume Kwankwaso.

A wasu hotuna da Hadimin Sanata Rabiu Kwankwaso mai suna Saifullahi Hassan ya fitar, an ga ‘dan siyasar tare da sauran manyan kasar nan a wannan taro da aka kuma daura wasu aure.

An yi bikin auren Njideka Edith da Dr.Ugochukwi Ybenga wadanda ‘Ya ‘ya ne wurin Cif Dr. Emeka C.O da kuma Lady Nkiru Rosemary Offor a wani katafaren otel da ke Legas duk a kwanan nan.

Wani bikin auren da aka yi a dakin taron otel din Skyline Terrace Oriental na Legas shi ne na Nathaniel Akujuobi da Adunni Chinyere Udu. An yi duk bukukuwan ne a Ranar 12 ga Okotoba.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel