Najeriya ta mikawa Amurka manyan motocin yaki da ta kama

Najeriya ta mikawa Amurka manyan motocin yaki da ta kama

Gwamnatin Najeriya a ranar Juma’a, 11 ga watan Oktoba, a Yola, ta mikawa gwamnatin Amurka motocin yaki guda shida wadanda aka kama a watan Agusta.

Sojojin Najeriya dake kula da tashar bincike a jihar Adamawa ne suka kama motocin da ake ganin an shigo dasu Najeriya ba tare da bin ka'ida ba.

Jami’an sojin dake aiki tare da Brigade 23 a Yola ne suka kama kayan yakin a karamar hukumar Fufore.

Ba a dai tabbatar da ko an kama wadanda suka shigo da motocin ba tunda haramun ne shigo da irin wadannan motoci ba tare da takardan shaida daga ofishin mai ba kasa shawara akan harkar tsaron ba, domin ita ce hukumar tarayya guda daya tak dake da ikon bada wannan takarda.

Bayan kama motocin, ya cigaba da kasancewa a hannun hedkwatar rundunar kwastam da ke Yola.

Mista Kamardeen Olumoh, Kwanturolan kwastam reshen Yola ne ya mika motocin a madadin gwamnatin Najeriya zuwa ga Kathleen FitzGibbon, mataimakin shugaban ayyuka a ofishin jakadancin Amurka a Najeriya.

Olumoh ya bayyana cewa rundunar ta samu umurnin sakin motocin daga wajen ofishin mai ba kasa shawara akan harkar tsaro.

A jawabin ta FitzGibbon ta gode ma gwamnatin Najeriya kan fahimtarta, inda ta kara da cewa motocin zasu Jam’uhiyar Nijar ne don aiwatar da aiki na tsaro.

KU KARANTA KUMA: Dalilin da ya hana sojojin Najeriya murkushe Boko Haram – Kwamanda

Ta kara da cewa rundunar sojin sama na Amurka za ta yi safarar motocin zuwa jumhuriyar Nijar.

NAN ta rahoto cewa an sa hannu a wasu takardu da dama yayin mika motocin.

Har ila yau NAN ta rahoto cewa taron ya samu halartan manyan jami’an sojoji daga kasashen biyu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng