Chamberlain: Magajin Shugaba Buhari ba ya cikin gwamnati amma ya na kusa da shi

Chamberlain: Magajin Shugaba Buhari ba ya cikin gwamnati amma ya na kusa da shi

Wata fitacciyar Malamar duba a Najeriya, Oby-Judith Chamberlain ta yi magana game da shugabancin kasar nan inda ta fadi wanda zai zama Magajin shugaba Muhammadu Buhari.

A wata hira da babbar Malamar ta yi da Legit TV, ta bayyana cewa wanda zai gaji shugaban kasa Buhari a kan mulki wani na-kusa da shi a halin yazu. Malamar ba ta kama sunan kowa ba.

Jagoran cocin na "Christ Anointing and Revival Ministry" na Najeriya ta ke cewa ba Fasto bane wanda zai karbi ragamar mulkin kasar nan a hannun Buhari wanda yake wa’adin karshe.

Wasu na tunanin mulki zai koma hannun mataimakin shugaban kasa watau Farfesa Yemi Osinbajo ne idan shugaba Buhari ya kammala. Osinbajo dai Fasto ne a cocin nan na RCCG.

Chamberlai wanda Malamar addini ce, ta hango cewa wanda zai yi mulki ba zai zama Takwaranta Fasto ba. Malamar ta kuma ce ko da jama’a za su soke ta, ba zai hana ta fadi abin da ta gani ba.

KU KARANTA: Fasto yace shi zai zama shugaban kasar Najeriya bayan Buhari

Wannan Baiwar Allah ta nuna cewa kafin a kai karshen mulkin nan, Duniya za ta gane wanda ake shirin mikawa kasar, kuma tace wannan mutumi ba ya aiki da shugaban kasar a halin yanzu.

Bayan cewa Mai jiran gadon ba ya cikin gwamnatin APC mai-ci, Fasto Oby-Judith Chamberlain ta kyankyasa cewa shugaban kasar goben ya na da kusanci da shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Faston ta kuma nuna cewa shugaban wani tsoho ne zai zo da kayan yara. Sai dai wannan bayani na ta ya na bukatar Masana su yi fashin baki kafin a fahimci ainihin tarin sakon da ya kunsa.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel