Jihohi 5 da suka fi kwazo a Najeriya - WAEC
Hukumar shirya jarabawar kammala makarantun sakandire ta Afirka ta Yamma wato WAEC, ta daraja jihar Kano a cikin sahun jihohi biyar da suka fi kwazo a jarrabawar da hukumar ta gudanar a bana cikin fadin kasar nan.
Mataimakin shugaban hukumar na Najeriya, Henry Adewumi, shi na furta hakan a ranar Talata yayin wani taron bunkasa harkokin ilimi da aka gudanar a harabar cibiyar kula da albarkatun ilimi ta jihar Kano, KERD.
A cewarsa kamar yadda jaridar Kano Focus ta ruwaito, sauran jihohin hudu da ke tarayya kan sahu guda da jihar Kano sun hadar da Abia, Legas, Bayelsa da kuma Nasarawa.
Mr Adewumi ya ce jihohin biyar sun samu mafi yawan adadin dalibai da suka yi nasarar samun 'Credit' biyar zuwa sama a darussa daban-daban da suka hadar da Turanci da kuma Lissafi.
KARANTA KUMA: Rashawa ce ta haddasa mugun talauci a Najeriya - Osinbajo
A nasa bangaren, shugaban cibiyar KERD, Nura Sani Yakasai, ya godiya ga hukumar WAEC musamman a kan yadda ta saki sakamakon jarrabawar dalibai a bana a kan kari, lamari daya ce hakan zai bai wa daliban damar neman shiga makarantun gaba da sakandire a lokaci da ya dace.
Sauran mahalarta taron sun hadar da wakilan kungiyar malaman Najeriya reshen jihar Kano, da kuma kungiyar shugabannin makarantun sakandire ta kasa.
A ranar Alhamis ne hukumar WAEC ta sanar da nadin sabon shugabanta, Mr. Pateh Bah dan kasar Gambia, wanda ya ci gajiyar kujerar a hannun Dr. Iyi Uwadiae bayan da wa'adinsa ya kare a ranar 1 ga watan Oktoban 2019.
Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:
https://facebook.com/legitnghausa
https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng