Kaduna: Masu garkuwa da mutane sun nemi fansar N10m kan kowace Yarinya

Kaduna: Masu garkuwa da mutane sun nemi fansar N10m kan kowace Yarinya

Wadanda su ka sace ‘Yan makaranta da Malamai daga wata Makarantar Sakandare mai suna Engravers College a Unguwar Kakau Daji da ke cikin karamar Chikun sun rage kudin da su ka sa.

Yanzu haka ‘yan mata shida da wasu Malamai 2 ne ke hannun wadannan masu garkuwa da mutane inda su ke bukatar Iyayen yaran su bada Naira miliyan goma kafin a saki wadannan ‘Ya ‘yan na su.

Haka zalika an nemi Iyalan Malaman makarantar su biya makamancin wannan makudan kudi kafin a sake su ga danginsu. A baya masu garkuwa da mutanen sun bukaci a biya su Naira miliyan 50 ne.

Daga cikin wadanda aka sace har da mataimakiyar shugabar wannan Makaranta da kuma wata Ma’aikaciya da ke kula da ‘yan makarantar. Daga cikin Yaran da aka sace akwai wasu ‘yan gida guda.

Wadannan Miyagu sun rage farashin da su ka sa ne a lokacin da su ka tuntubi Iyayen wadannan yara da dangin Malaman makarantar a wayar tarho. Sun ce dole a biya wannan kudi domin a saki yaran.

KU KARANTA: An kashe Sojoji fiye da 30 da masu fararen hula da-dama a Najeriya

Masu garkuwan sun nuna cewa ba su da sha’awar a biya kudin a dunkule, inda su ka hakikance a kan cewa kowane Iyaye su biya kudin ‘Ya ‘yan su. Jaridar Daily Trust ce ta samu wannan rahoto dazu.

“Sun fada mani cewa sun ji labarin sace yaran a BBC, don haka su ka kira ni su na ta surfafa mani zagi.” Wani daga cikin iyayen ya fadawa ‘yan Jaridar a farkon Ranar Litinin 7 ga Watan Oktoban 2019.

“Sun ce ba su son a biya kudin a dunkule. Kowane Iyaye su biya Naira Miliyan 10 domin su karbi ‘Yar su. Sun dauka ina tattaunawa da su ne a madadin gwamnati.” Inji wani daga cikin Iyayen Matan.

“Sun tambaye ni ko ni Lauya ne, na fada masu cewa ni Malamin makaranta ne. Su ka tambaya ko ni ne Mai makarantar. Daga nan na roki su cewa su yi hakuri su sake mani Yarinya don ba ni da kudi.”

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel