A karo na farko, Wammako ya yi magana a kan hukuncin da kotun zabe ta yanke a Sokoto
Jagoran jam'iyyar APC a jihar Sokoto kuma tsohon gwamnan jihar, Sanata Aliyu Wammako, ya ce APC za ta karbi kujerar gwamnan Sokoto a kotun daukaka kara.
Wammako, Sanata mai wakiltar jihar Sokoto ta Arewa a majalisar dattijai, ya fadi hakan ne ranar Asabar yayin da yake gabatar da jawabi ga magoya bayansa a gidansa da ke Sokoto, tare da bayyana hukuncin kotun da ya tabbatar da samun nasarar Tambuwal akwai kuskure a cikinsa.
A cewarsa, APC jam'iyya ce mai biyayya ga dokokin kasa, a saboda haka za ta cigaba da bin matakan shari'a domin ganin ta karbo hakkinta da jama'a suka bata.
"Ina mai tabbatar muku cewa zamu cigaba da neman hakkin mu da aka yi mana fashinsa, sai mun ga abinda ya ture wa buzu nadi.
"Jihar Sokoto ta jam'iyyar APC ce kuma har yanzu babu abinda ya canja, a saboda haka ina bukatar magoya bayan mu su kasance masu biyayya ga doka. Kwanan nan doka za ta warware komai dangane da haramben zaben da aka yi mana.
"Mu cigaba da yi wa jam'iyyar mu addu'ar samun nasara a jihar Sokoto da ma kasa baki daya," a cewar Tambuwal.
DUBA WANNAN: Mulki dole: Tsohon gwamnan APC daga arewa na ta hankoron Buhari ya nada shi shugaban FIRS ta kowacce hanya
A jawabin da ya gabatar, dan takarar kujerar gwamna a Sokoto a karkashon inuwar jam'iyyar APC, Ahmed Aliyu, ya yi jama'ar jihar godiya bisa goyon bayan da suke bashi da jam'iyyar APC.
A ranar 2 ga watan Oktoba ne kotun sauraron korafin zabe gwamnan jihar Sokoto ta yanke hukunci a kan karar kalubalantar sake samun nasarar gwamna Aminu Tambuwal a zaben gwamna da aka yi a watan Maris. Kotun ta tabbatar wa da Tambuwal nasarar da ya samu a zaben, tare da yin watsi da bukatar APC na neman a soke zaben.
Kotun ta yi watsi da bukatar APC da dan takarar ta Aliyu, bisa hujjar cewa zargin da suke yi bashi da tushe, saboda sun gaza gamsar da kotun cewa an yi musu magudi yayin zaben.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng