Sabon salo: An gyara titin wata jiha da kankare a maimakon kwalta

Sabon salo: An gyara titin wata jiha da kankare a maimakon kwalta

- Rahoto ya nuna cewa gwamnatin jihar Anambra ta yi amfani da kankare wajen facin titi

- Da manema labarai suka tunkari kwamishinan aiyukan jihar da zancen, sai yace ba su bane na farko da suka fara hakan

- Kwamishinan aiyukan ya ce, damuwar mutane akan lalacewar titunan jihar ne yasa suka samo mafita ta wucin-gadi

Rahoto ya nuna cewa gwamnatin jihar Anambra ta yi amfani da kankare wajen facin titi. Amma tambayar a nan itace, anya titin zai yi karko? Kuma menene dalilin amfani da kankare a maimakon kwalta da kowa yasan ana amfani da ita wajen gyaran titi?

A yayin da gwamnatin jihar ke bada amsoshin tambayoyin nan, ta ce ta yi amfani da kankare ne saboda mamakon ruwan sama da ake yi a jihar.

KU KARANTA: Abin Mamaki: Alkali ya harbe kansa ana tsaka da shari'a

Kwamishinan aiyukan na jihar, Marcel Ifejiofor, ya sanar da manema labarai a ranar juma'a cewa an yi amfani da kankaren ne na wucin-gadi ba wai dindindin ba don a samu saukin kai kawo a titunan har zuwa lokacin da damina zata wuce.

Kamar yadda ya fada, babu wani aibun amfani da kankare wajen gyaran titi.

"Yawan ruwan saman da ke sauka a shekaru uku da suka gabata abin a duba ne. Ba mu taba ganin irinsa ba a da. Kuma zan iya cewa titunan jihar Anambra sun fi na wasu jihohin," in ji kwamishinan.

Ya kara da cewa, "Eh, wasu daga cikin tutunanmu basu da kyau, amma gwamnatin Willie Obiano na da tsarin yin abubuwa da yawa akan hakan. Da yawan titunan da ba a iya amfani dasu, titunan tarayya ne, ko su muna gyaransu."

Ya ce, "Inaso in sanar in sanar da ku cewa, babu aibu a facin titi da kankare. Ku je tsuburin Victoria da ke Legas, da yawan titunansu anyi su da kankare ne. Ku je Eboyin, akwai tituna da aka yi su da kankare,"

"Maganganun da kafofin yada labarai ke yi akan halin da titunanmu ke ciki ya yi yawa, shiyasa muka nemi hanyar shawo kan matsalar na wucin-gadi." kwamishina ya ce.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel