Bafarawa: Kishin-kishin din da ake yi na tasirin Tinubu a APC ya na wargajewa

Bafarawa: Kishin-kishin din da ake yi na tasirin Tinubu a APC ya na wargajewa

Yayin da aka fara lissafin 2023 da kuma kokarin samun shiga da iko a jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya, tsohon gwamna Attahiru Dalhatu Bafarawa ya fito ya yi magana kan halin da ake ciki.

Alhaji Attahiru Bafarawa ya bayyana cewa abubuwan da ke faruwa a jam’iyyar APC su na kasancewa ne saboda rashin gaskiyar wasu daga cikin manyan jiga-jigan jam’iyyar mai mulki.

Bafarawa wanda tsohon‘dan siyasa ne a Najeriya, ya tuna yadda wata hira da ya yi da Bola Tinubu a shekarar 2008 a kasar Amurka ta yi sanadiyyar kafa APC wanda ta karbi mulkin kasar a 2015.

Kamar yadda mu ka samu rahoto, tsohon ‘dan takarar shugaban kasar yace APC ta fara kokarin yin sulhu da wasu da su ka samu sabani da su, jam’iyyar ta fara wannan ne domin shiryawa 2023.

Tsohon gwamnan na Sokoto yace wasu a jam’iyyar su na ganin sulhun da ake yi a matsayin kokarin dakile karfinsu a zabe mai zuwa. Bafarawa yace wannan ne salon APC tun da aka kafa ta.

KU KARANTA: An yi rigima tsakanin tsohon Sanatan APC da Mai ba Gwamna shawara

Bafarawa ya zargi Tinubu da kokarin janyo gwamnonin PDP zuwa APC a 2014, kuma daga baya aka mika jam’iyya a hannunsu duk da akwai manyan ‘yan siyasar da aka reni APC da guminsu.

Alhaji Bafarawa yake cewa APC ta damka jam’iyya a hannun wadannan gwamnoni 5 ne a lokacin domin ta kara samun karfin tattalin arziki, sai dai hakan ya yi wa shi da Ibrahim Shekarau illa.

Har ila yau, ‘dan adawar ya na zargin abin da ke faruwa a cikin APC yau a matsayin wani yunkuri na Bola Tinubu na karbe ikon jam’iyyar. Sai dai wasu sun ankara sun tashi tsaye a cikin tafiyar.

Attahiru Bafarawa yake cewa wadanda su ka farga da yunkurin Jigon na APC yake yi na ganin APC a kan tafin hannunsa, sun soma taka masa burki domin su samu gindin zama a zaben 2023.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel