Jerin sunayen jaruman Kannywood da suka barranta kansu da tsarin hukumar tace fina-finai a Kano

Jerin sunayen jaruman Kannywood da suka barranta kansu da tsarin hukumar tace fina-finai a Kano

A makon jiya ne wa'adin da hukumar tace fina-finai a Kano ta diba domin tantance masu sana'ar shirya fina-finai a jihar ya cika, lamarin da ya kawo karshen shirin tantance masu sha'awar yin sana'arsu da lasisi daga hukuma.

Rukunin masu sana'ar da hukumar ta sanar za a tantance sun hada da jarumai, mawaka, marubuta, darektoci, furodusoshi, masu daukan hoto da tace wa da sauransu.

An shafe tsawon sati hudu ana gudanar da tantancewar kuma abinda ya fi jan hankalin mutane shine wadanne manyan jarumai da darektoci ne suka gabatar da kansu domin a tantance su da kuma wadanda suka barranta kansu da tsarin.

A wani kiyasi da jaridar northflix.ng ta wallafa, ta ce mutane 600 sun yi rijista a matsayin jarumai, 77 a matsayin furodusoshi, darektoci 76, marubuta 40 sai kuma mutum 30 da suka yi rijista a matsayin masu daukar hoto. Alkaluman basu hada da na mawaka.

DUBA WANNAN: Hameed Ali ya zayyana dalilai biyu da suka sa FG ta rufe iyakokin Najeriya

Jaridar ta ce kusan dukkan manyan fitattun jarumai mata sun je an tantance su, in banda wasu fitattun jarumai da suka hada da Rahama Sadau, Aisha Tsamiya, Fati Washa, Hadiza Gabon da Nafisa Abdullahi. An ce wasu daga cikinsu sun kira tare da bayar da uzurinsu na rashin halartar tantancewar.

Alhassan Kwalle ya shaida wa wakilin northflix.ng cewa Rahama Sadau, Fati Washa, Hadiza Gabon, Nafisa Abdullahi da Ali Jita sun kira tare da bayar uzurin rashin ganinsu yayin tantancewar, lamarin da ke nuna cewa suna tare da tsarin tantancewar.

Kazalika, akwai wasu fitattu a masana'antar Kannywood da tun farko suka barranta kan su da tsarin tantancewar, daga cikin irin wadannan jarumai akwai; Adam A Zango, Sani Danja, Mustafa Naburaska, Falalu Dorayi, Aminu Saira, Sunusi Oscar 442, Yakubu Muhammad, Nazir Ahmad, Aminu Ala, Naziru M Ahmad, Misbahu M Ahmad, Baban Cinedu, Nuhu Abdullahi, Abdul Amart, Nasir Gwangwazo, Nazifi Asnanic da sauran su, kamar yadda northflix.ng ta rawaito.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng