Tabarbarewar tarbiyya: Yansanda sun kama karamin yaro dauke da daurin wiwi 46 a Katsina

Tabarbarewar tarbiyya: Yansanda sun kama karamin yaro dauke da daurin wiwi 46 a Katsina

Rundunar Yansandan Najeriya reshen jahar Katsina ta kama wani karamin yaro dan shekara 18, Abdullahi Lawal dake zaune a kauyen Nassarawa na karamar hukumar Dandumen jahar Katsina da laifin dillancin tabar wiwi.

Rahoton jaridar Punch ta bayyana cewa Yansandan sun kama Lawal ne dauke da daurin tabar wiwi guda 46 a ranar 13 ga watan Satumbar 2019 yayin wani samame da Yansanda suka kai wata mabuyar miyagun mutane.

KU KARANTA: Gwamnatin jahar Zamfara ta fara hada magunguna domin amfanin talakawa

Majiyar Legit.ng ta ruwaito a ranar Laraba, 18 ga watan Satumba ne kaakakin Yansandan jahar Katsina, SP Gambo Isah ya tabbatar da kama Lawal, inda yace tuni ya amsa ma Yansanda laifinsa, kuma a shirye suke su gurfanar da shi gaban kotu.

A wani labarin kuma, kaakakin Yansanda ya bayyana cewa sun kwato wata motar Toyota Highlander mai lamba RBC 434 JA mallakin wani mutumi Emmanuel Ayni da aka kwace masa a garin Zarian jahar Kaduna.

“A ranar 17 ga watan Satumba da misalin karfe 3:30 na dare Yansandan Danja suka samu labarin yan fashi sun kai hari gidan Emmanuel Ayni a rukunin gidaje na Graceland dake garin Zaria, jahar Kaduna, inda suka dauke masa mota suka kuma nufi hanyar Katsina.” Inji shi.

A wani labari kuma, Jami’an rundunar Yansandan Najeriya reshen jahar Legas sun samu nasarar cafke wata buduwar yar shekara 23 mai suna Stella Peter wanda ta kashe saurayinta, Bala Haruna mai shekaru 25 a rayuwa.

Stella ta kashe Bala ne sakamakon takaddama ya barke a tsakaninsu a gidansu dake lamba 2, layin Tejuosho, cikin yankin Surulere na jahar Legas, kamar yadda kaakakin Yansandan jahar, Bala Elkana ya tabbatar.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel