Wata dalibar jami’a ta kashe saurayinta akan N2,500

Wata dalibar jami’a ta kashe saurayinta akan N2,500

Wata dalibar jami'ar jihar Ekiti da ke Ado Ekiti, Bukola Odeyemi ta daba ma saurayinta dan shekara 22 wanda ya kasance shima dalibi ne a makarantar, John Iju wuka.

Matashin ya mutu ne a sakamakon daba masa wukar da tayi.

Wata majiya ta rahoto cewa lamarin ya faru ne a yankin Iworoko-Ekiti da misalin karfe 10:00 na daren ranar Litinin, a daya daga cikin dakunan kwanan da daliban jami’ar masu zaman kansu ke zama.

Dalibar yar shekara 20 wacce ke karantan fannin ilimin halitta ta samu sabani da saurayin nata ne sakamakon hana ta N2,500 domin tayi gyaran gashin kanta.

A cewar majiyar, masoyan biyu sun yi sa-in-sa sosai a tsakanin su akan lamarin kafin Misis Odeyemi ta daba mishi wuka.

Abokan marigayin ne suka kai karan lamarin ga ofishin yan sandan da ke Iworoko.

Sun ce ihun neman agaji da yayi ne yayi sanadiyar zuwansu inda lamarin ya faru.

KU KARANTA KUMA: Wani mutumi ya koka bayan tsallake rijiya da baya, yace wani malamin addini yayi masa biza na bogi

Kakakin yan sandan jihar Ekiti, DSP Caleb Ikechukwu yace, "An tabbatar da lamarin. An kama wacce ake zargin."

Ikechukwu wanda yace yan sanda sun soma gudanar da bincike kan lamain, yace za a gurfanar da mai laifin gaban kotu da zaran an kammala bincike.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel