Yan sandan Neja sun kama mutane 5 kan kisan wani da ake zargi da sace budurwarsa

Yan sandan Neja sun kama mutane 5 kan kisan wani da ake zargi da sace budurwarsa

Rundunar yan sandan Najeriya reshen Jihar Neja, ta kama wasu mutane biyar bisa zargin hada baki wajen aikata laifin kisan kai a karamar hukumar Kontagora dake jihar.

Kakakin rundunar yan sandan jihar, Muhammad Abubakar ne ya bayyana haka a wani jawabi a ranar Laraba, 18 ga watan Satumba, a Minna, babban birnin jihar.

Abubakar ya bayyana cewa a ranar 13 ga watan Satumba, 2019 da misalin karfe 2:00am ne yan sandan ‘B‘ Division Kontagora suka kama masu laifi biyar kuma mambobin ‘Yan Kwamiti da hukumar Hisba bisa laifin kishe wani mai suna Ibrahim A. Ibrahim.

An zargi Ibrahim da alhakin sace budurwarsa mai suna Maryam Salmanu da ke yankin Unguwan Yamma a Kontagora.

Abubakar yace tawagar yan sanda daga ‘A’ Division Kontagora sun kama masu laifin wadanda sunansu yake kamar aka; Ahmadu Yahaya, 35; Dahiru Abdullahi, 28; Abdulrasheed Atabo, 20; Yunusa Adamu, 22 da kuma Abubakar Usman 20, duk sun kasance mazauna yankin Anguwan Yamma da ke Kontagora.

Yace a lokacin bincike, an gano cewa masu laifin sun azabtar da Ibrahim, suka kuma yi mishi rauni wanda hakan yayi sanadiyyar mutuwarsa.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Sojoji da yan sanda sun mamaye ofishin Sahara Reporters a Lagas

Kakakin yan sandan ya shawarci kungiyoyin yan banga, Yan Doka, Yan Sakai da dukkan hukumomin bada agaji da su gudanar da ayyukansu kamar yanda doka ta tanada don taimaka ma kokarin da yan sanda ke yi wajen kare rayuka da kaddarori.

Abubakar ya bayyana cewa za a gurfanar dasu a kotu bayan an kammala bincike.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel