Aisha Umar Ardo ta dawo gida bayan an biya masu garkuwa kudin fansa

Aisha Umar Ardo ta dawo gida bayan an biya masu garkuwa kudin fansa

Mun samu labari cewa an saki ‘Diyar Dr Umar Ardo wanda aka sace Ranar Asabar da ta wuce a Abuja. Umar Ardo ya bayyana cewa sai da ya biya kudi masu yawa sannan aka saki Yarinyar.

Umar Ardo ya shaidawa Daily Trust cewa wadanda su ka saci Yarinyar, sun tuntube sa a safiyar Ranar Lahadi inda su ka tabbatar masa da cewa za su sake ta idan har ya yi abin da su ke bukata.

Ardo yake cewa da su: “Zan amince da bukatun ku mu yi sulhu amma a kan sharadi daya; za ku cika mani alkawura biyu; Ba za ku yi wa ‘Diya ta illa ba, watau ma’ana ba za su ka kashe ta ba.”

Babban ‘dan siyasar na Adamawa ya kuma gindayawa masu garkuwa da ‘Diyar ta sa cewa: “Na biyu shi ne ba za ku keta alfarmar ‘Diya ta ba, da haka ina nufin cewa ba za ku yi mata fyade ba.”

Tsohon ‘Dan takarar na PDP ya ce ya fadawa wadannan Miyagu cewa idan har ba za su iya cika wannan alkawura ba, to su tafi su je su yi duk abin da su ka ga dama da wannan Baiwar Allah.

Wanda ke tsare da Yarinyar ya fada masa ta wayar salula da su ke zantawa cewa: "Dr., na ga alamar cewa kai Dattijo ne, ni ma Dattijo ne. Na yi maka alkawarin ba za mu taba ‘Diyar ka ba.”

KU KARANTA: An saki wasu da aka yi garkuwa da su a Jihar Katsina

Umar Ardo yace daga nan ya tambaye su abin da su ke bukata, sai su ka fada masa cewa zai tura masu kudi Dala $15, 000. Masu garkuwan su ka fada masa cewa idan ya saba za su kashe yarinyar.

Masu garkuwan sun nemi a biya wannan kudi ne da bitcoins inda ya fada masu bai san kan sa ba, A haka su ka koya masa yadda zai yi, ya kuma tura masu Dalolin daga asusun kudin kasar wajensa.

Bayan dogon lokaci da aika masu wannan kudi, sai su ka sanar da shi cewa ya zo ya dauki ‘Diyarsa a wani wuri da ake kira Drumstick a Unguwar Gwarimpa, inda duka gidan su ka fita su ka ceto ta.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel