'Yan bindiga sun kashe Muhammad Bayero, basarake a karamar hukumar Mangu

'Yan bindiga sun kashe Muhammad Bayero, basarake a karamar hukumar Mangu

Wasu 'yan bindiga da ba a san ko su waye ba sun kai farmaki fadar dagacin garin Kadunu, Muhammad Bayero, da ke masarautar Langai a yankin karamar hukumar Mangu ta jihar Filato.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa 'yan bindigar sun kashe basaraken mai lakabin 'Rit Kadunu' da misalin karfe 8:10 na dare yayin da suka harbi wani mutum guda a kafa.

Da yake tabbatar da kai harin, tsohon kwamishinan kasuwanci da masana'antu a jihar Filato, Honarabul Yakubu Idi Usman, ya ce an binne marigayi Bayero bisa tsarin addinin Islama da safiyar ranar Litinin.

Honarabul Usman ya ce akwai kyakyawan zaton cewa 'yan bindigar sun kai farmaki fadar ne domin su kashe Basaraken, saboda sun harbe shi fiye da sau daya.

DUBA WANNAN: A'iShat Umar Ardo: 'Yan bindiga sun sace diyar dan uwan Atiku a Asokoro

Da yake tabbatar wa da jaridar cewa 'yan sanda sun ziyarci fadar kuma sun nemi dukkan shaidu da bayanan da suke bukata, honarabul Usman ya kara da cewa; "yanzun nan na dawo daga wurin jana'izarsa."

Tsohon kwamishinan ya ce marigayin tamkar dan uwa ne a wurinsa tare da bayyana kisan da aka yi masa a matsayin babban abin takaici da bakinciki.

Daily Trust ta ce rundunar 'yan sandan jihar Filato bata fitar da wata sanarwa a hukumance ba dangane da mutuwar basaraken. Kazalika, jaridar ta bayyana cewa kakakin rundunar 'yan sandan jihar, DSP Tyopev Terna, ya ce yana tsaka da wani aiki a lokacin da wakilinta ya tuntube shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel