Gwamnonin PDP 4 sun kauracewa taron jam'iyyar na reshen Kudu maso Gabas

Gwamnonin PDP 4 sun kauracewa taron jam'iyyar na reshen Kudu maso Gabas

Gwamnonin jam'iyyar PDP hudu ne suka auracewa babban taron jam'iyyar na reshen Kudu maso Gabashin Najeriya da aka gudanar a jihar Anmabra.

Kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito, gwamnonin da suka kauracewa taron sun hadar da na jihar Imo, Emeka Ihedioha, gwamna Okezie Ikpeazu na jihar Abia, gwamnan jihar Enugu, Ifeanyi Ugwuanyi, da kuma gwamnan jihar Ebonyi, Dave Umahi.

Sai dai babu shakka shugaban jam'iyyar PDP reshen Kudu maso Gabashin Najeriya, Austine Umahi da manema takarar gwamnan jihar Anambra na zaben 2021 sun halarci taron da suka hadar da Dr Obiora Okonkwo, Sanata Uche Ekeunife da kuma Chris Azubuogu.

A yayin da suka daura damarar aiwatar da salon siyasa ba tare da adawa da juna ba, dukkanin manema takarar sun sha alwashin tabbatar da jam'iyyar PDP ta mamaye yankin Kudu maso Gabashin Najeriya a 2021.

A wani rahoton da jaridar Legit.ng ta ruwaito, gwamnonin babbar jam'iyyar hamayya a Najeriya ta PDP, sun gargadi gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, da ya kiyaye lafuzansa tare da kauracewa sukar takwarorin jam'iyyarsa.

A yayin da gwamnonin ke neman gwamna Wike da ya kame bakinsa wajen suka da caccakarsu, sun nemi da ya basu hadin kai wajen kwatar mulkin kasar daga hannun jam'iyya mai ci ta APC.

KARANTA KUMA: SON ta rufe kamfanonin man-juye 10 a jihar Kano

Rahotanni sun bayyana cewa, wannan kira na gwamnonin jam'iyyar PDP na zuwa ne yayin da suka ziyarci gwamna Wike a ranar Juma'ar da ta gabata cikin birnin Fatakwal na jihar Ribas, inda suka jaddada tsayuwar dakan su a kan wannan lamari.

Tawagar gwamnonin bisa jagorancin gwamnan jihar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal, ta hadar da na jihar Umaru Fintiri na jihar Adamawa, Emeka Ihedioha na jihar Imo, Seyi Makinde na jihar Oyo, Samuel Ortom na jihar Benuwe da kuma Muhammad Bello Mutawalle na jihar Zamfara.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel