Wata sabuwa: Inda za a koma cin naman mutum da za a samu sauyin yanayi a duniya - Wani masani ya bayar da dalilin shi

Wata sabuwa: Inda za a koma cin naman mutum da za a samu sauyin yanayi a duniya - Wani masani ya bayar da dalilin shi

- Wani farfesa ya bada shawarar shi akan cewa mutane su koma cin naman mutane 'yan uwansu domin hakan shine zai kawo sauyin yanayi a duniya

- Farfesan ya bayyana hakan ne a wajen wani taro da ya halarta, inda ya ce inda mutane za su yi la'akari da maganar shi da ba karamin cigaba za a samu ba

- Da aka tambayeshi ko zai iya cin naman mutum, ya ce kwarai kuwa zai iya gwada ci koda kadan ne

Wani masani a fannin kimiyya da fasaha dan kasar Sweeden ya bayar da wata hanya da za a dinga samun sauyin yanayi wacce ta bawa kowa mamaki a lokacin wani taro da aka yi a wata makaranta satin da ya gabata.

Mutumin mai suna Magnus Soderlund, wanda yake farfesa ne a fannin tattalin arziki, ya ce ya yadda cewa cin naman mutum wanda ya mutu, zai taimaka matuka wajen ceto al'umma idan har mutane suka yi la'akari da hakan.

Wasu daga cikin abubuwan da aka tattauna da farfesan sun hada hanyar da za abi domin inganta rayuwar al'umma, da kuma yiwuwar cin naman mutum idan zai kawo cigaba a duniya nan gaba.

KU KARANTA: Tashin hankali: Mai gadi ya kashe ubangidansa ya jefa gawar a cikin tankin ruwa

Da aka tambayeshi a lokacin da ake hirar da shi, idan har zai iya cin naman mutum, Soderlund ya ce yana ta tunani akan wannan lamarin.

"Ban san yadda zance muku ba akan wannan maganar, amma ina ganin zan iya gwada ci ko yaya yake," in ji shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel