Aikin Hajji: Jirgin Max ya kusa fadi da Maniyyata a Garin Minna

Aikin Hajji: Jirgin Max ya kusa fadi da Maniyyata a Garin Minna

Wani babban jirgin Boeing 744 mai lamba 5N/ DBK wanda ke dauke da wasu daga cikin Mahajjatan jihar Neja a Najeriya ya yi durar gaggawa wanda ya sa cikin mutane ya duri ruwa.

Kamar yadda mu ka samu labari daga Daily Trust, wannan jirgi na Boeing mai dauke da mutane 579 ya samu matsala ne a filin jirgi bayan ya taso Ranar Asabar da kimanin karfe 04:55 na Asuba.

Matsalar da jirgin saman ya fuskanta ya sa dole ya dura babu shiri a babban filin jirgin saman nan na Garin Minna da ke Saudi jim kadan bayan ya baro Birnin Jiddah inda ya dauko Mahajjatan.

Wani sashe na filin sauka da tashin jirgin saman ya kurje bayan sulbewar da jirgin ya yi wajen tashi sama. Wannan kuma ya jawo wani bangare na katafaren jirgin na Boeing ya samu matsala.

A cewar wani da abin ya faru a idanunsa, wannan matsala da aka samu ya jawo wasu fasinjoji biyu sun sume. Mutane da yawa sun shiga karanta Kuru’ani ne bayan jin karar da jirgin ya rika yi.

KU KARANTA: Alhazan Jihar Kaduna kaf sun dawo gida bayan aikin Hajjin bana

Hajiya Asabe, wata Baiwar Allah da ta sauke farali ta jihar Neja ta sanar da Daily Trust cewa wasu mata uku sun shiga gargara a sakamakon wannan abu da ya faru da wani fiffike na jirgin saman.

A karshe dai an yi dace komai ya dawo daidai bayan mutane sun yi ta faman ihu da salati da addu’o’i ko ta ina. An zarce da wadanda su ka samu matsala zuwa asibiti a cikin Garin Minna.

Wani jami’in jirgi a Najeriya ya tabbatar da cewa babu shakka za a binciki duk abin da ya faru a Abuja. Tuni ma har an soma duba ainihin lamarin inda ake zargin Matukin wannan jirgin da laifi.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel