Hajjin bana: Jihar Kaduna ta kammala kwaso alhazanta daga kasa mai tsarki

Hajjin bana: Jihar Kaduna ta kammala kwaso alhazanta daga kasa mai tsarki

Rahotanni sun kawo cewa an kwaso rukunin karshe na Alhazan jihar Kaduna da suka shiga jerin wadanda suka yi aikin hajjin bana na 2019, a kasar Saudiyya. Mahajjatan sun dawo ne a yau Asabar, 7 ga watan Satumba.

A wani jawabi daga jami’in hulda da jama’a na hukumar aikin hajji a jihar Kaduna, Yunusa Muhammad Abdullahi, ya bayyana cewa a rukunin karshen, alhazai 390 ne suka isa Kaduna da misalin karfe 1:01 na ranar Asabar, a ikin jirgin kamfani Nas Airline.

Darakta Janar na kungiyoyin addini, Sheikh Jamilu Abubakar Albani, Shugaban hukumar, Imam Hussaini Sulaiman Tsoho Ikara da sauran jami’an gwamnati duk sun kasance a cikin jirgin karshe, cewar jawabin.

Abdullahi yace jirage biyu, Med-View da Fly Nas ne suka yi jigilar mahajjatan jihar Kaduna a wannan shekarar, inda ya kara da cewa a lokacin dawowarsu, Max air tayi jigilar Alhazai 2,710 yayinda Fly Nas ta kwaso alhazai 834.

KU KARANTA KUMA: Matasa a Kano sun yi zanga-zangar lumana kan hare-haren Afrika ta Kudu

A cewar jawabin, mahajjata 3,544 ne suka yi hajjin bana daga jihar Kaduna inda mutum guda ya mutu a Makkah.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel