Babban magana: Wani mutumi ya bace bat bayan ya nuna wa malaminsa sabuwar motar da ya siya

Babban magana: Wani mutumi ya bace bat bayan ya nuna wa malaminsa sabuwar motar da ya siya

Jami’an yan sanda na Operation Puff Adder a jihar Imo sun kama wani limamin coci dan shekara 27 mai suna Mbonu Micheal kan haddasa batan wani mabiyin shi, Princewill Ezeji.

An tattaro cewa Ezeji ya siya sabon mota sannan ya je nuna wa limamin cocin domin ya sanya masa albarka a motan, amma sai aka neme shi aka rasa sannan bayan mako guda sai aka tsinci gawarsa.

A cewar jami’in hulda da jama’a na rundunar, SP Orlando Ikeokwu, “a ranar 6 ga watan Satumba, da misalin karfe 11:00, wani mutum mai suna Emeka Ezeji ya kai wa rundunar rahoto game da batan dan uwansa mai suna Princewill Ezeji.

Ya bayyana cewa marigayin ya siya wata mota kirar Camry mai dauke da lamba WER 34 GL, sannan ya je nuna wa malaminsa (Mbonu Micheal) kuma tun daga lokacin ba a sake jin labarinsa ba kuma ba a waje ganinsa ba.

Ikeokwu yace da aka kama limamin cocin, sai ya jagoranci jami’an tsaro zuwa dajin da suka gano gawar mutumin, mota, waya, layinsa, bibu da kuma kayan asiri.

An kuma kama wasu mutane hudu da ke da nasaba da lamarin.

KU KARANTA KUMA: Yan sanda sun kama sojan da ya soki wani bawan Allah har lahira

Ikeokwu ya bayyana cewa wadanda ake zargin sun amsa tambayoyi sannan kuma za a mika su kotu.

Marigayin ya fito daga yankin Umunakolu da ke karamar hukumar Ehimem Mbano, Imo amma yana zama a Amawire Orji, duk a garin Owerri.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng