Saudiyya ta ba Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje lambar yabo

Saudiyya ta ba Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje lambar yabo

Mun samu labari cewa wata kungiya da ke lura da sha’anin aikin Hajji da Umrah a Duniya mai suna “Hajj and Umrah Forum” ta karrama gwamnan jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje.

Labarai24 ta rahoto cewa Sheikh Ibn Muhammad shi ne wanda ya ba gwamnan na Kano wani hatimin Al-Qur’ani mai dauke da rigar dakin Ka’aba mai tsarki a matsayin lambar yabo na musamman.

Ibn Muhammad ya ba Mai girma Abdullahi Ganduje wannan kyauta na karamci ne a madadin kungiyar ta Hajj and Umrah Forum saboda irin kokarin da gwamnatin jiharsa tayi wajen aikin hajjin bana.

Tsare-tsaren gwamnatin jihar Kano game da Alhazanta wajen aikin Hajjin wannan shekarar ne ya kayatar da wannan kungiya ta Duniya. Ganduje ya karbi kyautar ne ta hannun wani babban jami’in jihar Kano.

Kamar yadda rahotanni su ka bayyana, Abba Muhammad Ɗambatta, wanda shi ne Sakataren zartawar hukumar da ke kula da jin dadin Alhazai, shi ne ya karbi wannan lamba a madadin mai girma gwamna.

KU KARANTA: Najeriya ta dauki matakin farko bayan an kai wa mutanenta hari a kasar waje

An mikawa Abba Muhammad Ɗambatta wannan lambar yabo ne a Birnin Jiddah da ke Saudi Arabia. Muhammad Ɗambatta ya ji dadin karbar wannan kyauta inda ya yabawa shugabannin wannan kungiya.

Sakataren zartarwar na hukumar kula da aikin Hajjin na Kano ya yi alkawarin cewa gwamnatin jihar za ta kara kaimi wajen ganin Alhazan ta sun samu kulawa da walwalar da ta kamata wajen sauke farali

Shugaban hukumar kula da Alhazai na Kano, Abdullahi Saleh Pakistan, ya taya gwamna Abdullahi Umar Ganduje wanda ake kira Khadimul Islam murnar wannan shaida da ya samu.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel