Cristiano Ronaldo ya yi wa Lionel Messi tayin zaman shan shayi

Cristiano Ronaldo ya yi wa Lionel Messi tayin zaman shan shayi

Fiye da shekaru goma kenan Duniyar kwallon kafa ta na kallon taurarin Cristiano Ronaldo da Lionel Messi su na haskawa babu kautawa. Sai dai wadannan Taurari ba Abokan juna bane.

A karshen makon jiya ne kungiyar UEFA ta zabi ‘dan wasan Liverpool, Virgil Van Dijk a matsayin babban ‘Dan wasan Duniya na shekarar 2019 wanda ya sha gaban Lionel Messi da C. Ronaldo.

A Ranar Alhamis 29 ga Watan Agusta, 2019, Cristiano Ronaldo, ya yi wani jawabi da ya bada mamaki inda ya nemi a samu wata rana da shi da Lionel Messi za su zauna su abincin dare tare.

"Babu shakka, mu na da alaka mai kyau. Amma ba mu taba zama mun ci abinci tare ba tukuna, ina sa rai wata rana nan gaba za a yi haka.” Inji Ronaldo.

Ronaldo ya ce: “Ya tunzura ni, ni ma na kan tunzurasa. Abin alfahari ne shiga cikin tarihin kwallon kafa, ina cikin littafin tarihin kwallo, haka shi ma (Messi).

KU KARANTA: Ronaldo ya bayyana lokacin da zai ajiye kwallon kafa a Duniya

Shekaru kusan goma Ronaldo ya shafe a kasar Sifen inda ya buga wasa a Madrid, yayin da Lionel Messi ya ke Barcelona. Bayan komawar Ronaldo kasar Italiya, ya nemi yanzu ya zauna da Messi.

A cikin ‘yan shekarun nan, Duniyar kwallon kafa ba ta gamu da Taurarin da su ka hana kowa sakat ba irin Cristiano Ronaldo da Lionel Messi. Daga 2018 zuwa yanzu, sai da su ake damawa.

Idan har Ronaldo da Takwaran na sa na kasar Argetina su ka hadu a saman teburi guda su ka ci abinci, wannan zai zama karon farko da manyan 'yan wasan Duniyar ke haduwa a wajen fili.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel